mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Ni Dalibar ilimin addini ina fuskanta matsaloli masu tarin yawa da suke bijirowa kan hanya ta

Hanyar tsarkake zuciya: Ni Dalibar ilimin addini ina fuskanta matsaloli masu tarin yawa da suke bijirowa kan hanya ta shin ko akwai wata nasiha da nusantarwa zaku bani domin shiga wannan hanya, ko kuna da wani wuridi da kuka sani da zai taimaka cikin haddace karatuttukan fikihu da tantancewa da rashin mantuwa. ... Ganin amsa

Shin akwai wata `yar gajeriya kaifiyya la’ana da sallama cikin ziyarar Ashura

Hanyar tsarkake zuciya: Samahatus Assayid Adil-Alawi Allah ya daukaka mukaminka da sha’aninka ya kuma datar da kai ga soyayyarsa da kusanci ya tabbatar da mu da ku a kan hanyar gaskiya.. lallai shi mai Ji ne mai amsa addu’a.
Shin akwai wata gajeriya kaifiyar karanta la’ana da sallama cikin ziyarar Ashura? Shin karanta kafa daya yana isarwa musammam idan ta kasance da niyyar neman biyan bukata..?
Sakamakon kasantuwarmu masu neman gaskiya kololuwar burinmu gaskiya da kaiwa ga Allah shine hadafinmu, lallai zukatanmu sun damfaru da turakun Al’arshin Allah mai girma, ... ... Ganin amsa

Bani da Malami ina kuma gashi ina son in yi suluki cikin hanyar irfani na bincika sosai amma ban samu abin da zai taimakani zuwa ga wusuli ba

Hanyar tsarkake zuciya: Salamu Alaikum
Ban samu Malami ba kuma ina tsananin kaunar kutsawa cikin Irfani, hakika na bincika matuka amma ban ci karo da wani abu da zai kai ni zuwa ga wusuli ba, kawai ian dauka daga wannan littafi da wancan inyi aiki da abinda yake ciki tsawon kwanaki 40 sai dai cewa tareda haka ina jin shu’uri ina kewaye a wuri guda ne babu wani abu sabo gareni face kowacce rana ina samun Karin damfaruwa da kauna zuwa ga wusuli ga Allah ta’ala.
Ina rokonku ku taimaka mini.
Allah ya tsarkake lokutanku da ambaton Muhammad Alayensa amincin Allah ya tabbata a gareshi da Alayensa.
... Ganin amsa

Wanne ayyuka ne da ayoyi ne zasu taimaka mini kan kubuta daga sihiri

Hukunce-hukunce daban-daban: Salamu Alaikum
Assayid ina gaisuwa Allah ya saka muku da dubun alheri, wanne ayyuka da addu’a me za su taimaka kan kubuta daga sihiri, kari kan haka ina son yin wata tambaya: shin karanta suratu Yasin a kowacce rana yana da fa’ida kan wannan lamari da kuma dukkanin bukatu, sannan shin da gaske lazimtar karanta suratu Yasin yana bukatar izini, idan hakane shin zaku bamu izini.
Allah ya datar daku.
... Ganin amsa

Barin karatun Hauza

Hukunce-hukunce daban-daban:
Na kasance a baya na shagaltu da neman ilimi ina ta burun a bude kofar yin rijista domin in shiga Hauza ilimiya sai dai cewa kuma lokacin da aka bude kofar rijista na shiga na yi karatu ciki tsawon wani lokaci sai na samu kaina ba zan iya cigaba da karatun ba sabida yanayin rayuwa da rashin samu iko daga dangina ba zasu cigaba da taimaka mini ba, dole na koma gid ana bar karatun Hauza,
Tambaya anan shin wannan abu da nayi zai kasance daga aikin Shaidan Kenan, shin Shaidan yana katsalandan cikin irin wadannan lamurra yanzu yay azan gyara lamarin?
... Ganin amsa

Wasu daga cikin tambayoyi

Tura tambaya