mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasiwasi kan alwala da wanka da kuma sallah

Ni na kasance ina da yawan wasiwasi cikin alwala da wanka da kuma sallah, kuma ina da yawan tunace tunacen banza musamman lokacin bacci, ina kokarin wurin barin irin wannan tunani na banza amma ban samin nasara, don haka nake neman hanya da ataimaka min da hanya ma daidaiciya wanda zan sami nasara

Da sunan Allah me rahama me jin kai

An taba samin imam maasum da irin wannan matsalar, sai imam yake tambaya me yasa baya wasiwasi akan zakkar sa, cewa ya biya sau biyu ne, ko sau uku? Ko kuma me yasa baka wasiwasi kan humusin ka sai ka biya kudin humisin har iya yawan wasiwasin da kake da shi akan alolar ka ko kuma sallar ka domin da kana haka akan dukiyar ka da ka kasance mutum me gaskiya akan ayyukan ka.

والله المستعان

………………………………….

Hanyoyin barin wasiwasi

Na farko: yawaita addu’o’I da kuma tawassoli

Na biyu: tawakkali da Allah

Na uku: neman tsari daga shaidan da dakarunsa wanda daya daga cikin su shine waswaas, wanda ke sanya wasiwasi a cikin zukatan mutane

Na hudu: ne man karfafa aradan dan adamtaka me karfi wanda take galba akan shaidan.

Na biyar: ake daukan darussa da ga tajribobi, da zaka bar waswasi sau uku ko da ba da son ran ka bane shaidan yakan nisanta da ga gare ka amma idan ka bar waswasi na tsawon kwanaki uku a jere shaidan zai guje ka da izinin Allah

Na shida: a yawaita karanta wannan adduar ko da acikin Alqunuti ne

(اعوذ بالله القوي وبمحمد الرضي من شر الشیطان الغوي برحمتک یا ارحم الراحمین)
Tarihi: [2016/8/7]     Ziyara: [4002]

Tura tambaya