mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wadannan abubuwa ne ke zama alamun balaga ga `ya mace da namiji?


Daga cikin alamomin balaga ga maza da mata sune:
1-tsirar gashi a mara
2-fitar maniyyi a farke ko cikin mafarki da makamatansu
3shekaru wanda ga `da namiji shine kammala shekara 15 bisa lissafin kamariyya, mace kuma kammala shekaru tara 9 ita bisa lissafin watan kamariya.
Tambaya anan shi ne shin wadannan alamomin da ake dogaro da su cikin bayyana iyakance shekarun taklifi, ko kuma akwai wasu alamomin daban, kamar misalin ganin jinin haila da sauransu?
Tambaya ta biyu: idan daya daga cikin wadannan alamomi ta tabbata ragowar kuma basu tabbatu ba? misali idan namiji ya kammala shekaru 15 a lissafin hijira kamariya ita kuma mace tara 9 sai dai kua cewa ragowar alamomin basu tabbatu ba daga tsirar kakkausan gashin mara haka babu karfin iya jima’i ko kuma maniyyi bai fito ba, shin balaga tare da haka ta tabbatu ga su biyun?
Tambaya ta uku: shi ne idan mace da namiji suka iya samun karfin yin jima’i da fitar da maniyyi ta hanyar mafarki ko a farke sai dai cewa tareda tareda haka dukkaninsu babu wanda shekarun balagarsa na taklifi da akai ishara zuwa gare su ta kammalu?
Tambaya ta hudu: shin wajibi sai dukkanin alamomin da akai ishara da su sun tabbatu balagar taklifi ke tabbata ko kuma idan daya daga ciki ta tabbata ya isar?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

1-ya isar cikin shekarun taklifi idan daya daga cikin alamun ta tabbata.

2-balaga na tabbata koda daya daga cikin alamomi ne

3-da gundarin fitar maniyyi tare da sha’awa lallai hakan na nuni zuwa ga balagar shari’a daga nan ibada za ta fara wajaba kansu.

Tarihi: [2018/1/21]     Ziyara: [10063]

Tura tambaya