mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Me yasa malaman fikihu ke kokarin baiwa ra’ayoyinsu da ijtihadinsu tsarki

Lallai mu mun san cewa taklidi shi ne jahili ya tuntubi malami cikin ayyananniyar mas’ala da niyyar kawar jahilicinsa daga mas’alar, sai dai cewa mene ne ya sanya malaman fikihu ke kokarin baiwa ra’ayoyinsu da ijtihadinsu tsarki, mene ne ya sanya suke baiwa kawukansu gaskiya? Shin akwai wani yankakken dalili daga shari’a da ke shiryarwa kan muyi riko da ijtihadin wani mutum wanda bai da hujjantaka?

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Wannan bawai kokari bane kadai dai hakika ce daga tabbatattun abubuwa hakan ya kasantu ne tare da la’akari da dalilan fikihu wanda sune littafin Allah da sunna dukkanin biyun suna daga mafi tsarkakar tsarkakakku a wajen musulmai, idan shimfida ta kasance tsarkakka tabbas natijarta zata kasance tsarkakka, na’am akwai abu guda da ya rage shi ne cewa mu shi’a munyi imani da kuskure sabanin wadanda suke tafi kan dacewa dari bisa dari daga yan’uwanmu sunna, ma’ama dai shine munyi imani cewa mujtahidi fakihi yana iya yin kuskure cikin tsamo hukunci daga littafin Allah da sunna, kuma yana iya dacewa, idan ya dace to yanada lada biyu ladan wahala da ya sha da kuma ladan dacewa da abinda yake a littafin Allah da sunna, idan kuma ya kuskure to yanada lada guda `daya, kan wannan ne fikihu ya kasance tsarkakka ijtihadi ya ksance tsarkakakke.

Amma batun komawa wajen mafi sani wannan abu ne da hankali da lafiyayyar dabi’ar halitta ke  hukunci kansa, hakika na kawo bayani dalla-dalla cikin littafin (alkaulul rashid fi ijtihadi wat’taklid) cikin mujalladai uku a sauke a sayit sai ka koma zuwa gare shi.  

Tarihi: [2018/1/22]     Ziyara: [1021]

Tura tambaya