mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Barin karatun Hauza

Na kasance a baya na shagaltu da neman ilimi ina ta burun a bude kofar yin rijista domin in shiga Hauza ilimiya sai dai cewa kuma lokacin da aka bude kofar rijista na shiga na yi karatu ciki tsawon wani lokaci sai na samu kaina ba zan iya cigaba da karatun ba sabida yanayin rayuwa da rashin samu iko daga dangina ba zasu cigaba da taimaka mini ba, dole na koma gid ana bar karatun Hauza,
Tambaya anan shin wannan abu da nayi zai kasance daga aikin Shaidan Kenan, shin Shaidan yana katsalandan cikin irin wadannan lamurra yanzu yay azan gyara lamarin?

Salamu Alaikum.

Da sunan Allah Mai rahama mai jin kai

Lallai Shaidan jefaffe makiyi ne gad an Adam musammam ma Mumini, lallai Shaidan yana katsalandan cikin dukkanin abinda zai jawo mutum tsiyata da batarda shi da halakar da shi, lallai shi baya son alheri ga Mumini, tana iya ya kasance alherin rayuwarka yana cikin neman ilimi da karatun Hauza toi kaga ba zai kyaleka ba dole ya sanya maka kayoyi a hanya ya dinga yi maka wasiwasi, sannan ya bi mataki na biyu haka ya dinga kawo maka sawwale sawwale  sannan ya zo maka da miyagun akidu gurbatattu sai ya batar da kai daga tafarki na daidai ya koraka zuwa wuta, sannan daga karshe ya barranta daga gareka kamar yanda ya zo cikin suratu A’araf ka duba.

Amma yaya zaka gyara to kayi tawassuli da Allah kaji tsoran Allah hakikan tsoransa hakika zai shiryarka da kai hanya da tafarki.

(wadanda suka yi kokarin cikin lamarinmu zamu shiryar da su hanyoyinmu)

Ku ji tsoran Allah zai ilimintar da ku. Allah shine mafi alherin mai koyarwa da tarbiyantarwa shine mai tarbiyar talikai ka nemi taimakonsa ka dogara da shi kayi watsi da duk wata damuwa, ka sabunta tsaftacciyar rayuwa da Imani da aiki nagari.

Allah ne mai taimako.

Tarihi: [2021/5/23]     Ziyara: [483]

Tura tambaya