mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin akwai wani zikiri ko wani aiki da zai mini maganin yawan ciwon damuwa


Salamu alaikum
Shin inada wani zikiri ko wani aiki ayyananne da zai warkar dani daga ciwon yawan damuwa, musammam ma ya wayi gari yana tasiri cikin rayuwata ta yau da gobe, tareda tacewar soyayyata gareku da kaunata da girmamawa.

 

بسم الله الرحمن الرحیم

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Kayi watsi da yawaice-yawaicen sa damu a ranka ka fari sabuwar rayuwa wannan shi ne suna da taken littafin wanda daili karilji ya rubuta shi nayi mudala’ar littafin lokacin samartakata a kasar iraki a wannan lokaci na dauke shi abu kyau gareni duk da cewa akwai bukatuwar yin tsokaci a wasu ba’arin wurare, jigo cikin tunkude damuwa shi ne ka bincika sabubban da dalilan da suke kawo shi sai kasansu ka tunkude su a wannan lokaci idan sababi ya kare to abin da ke biyo bayansa ma yana tafiya ya kauce, amma idan illa da sababi suna nan to fa abin da ke biye da su bai rabuwa da su matukar suna nan samammu, ta yiwu ma shi yin zikirida wuridi yaki amfanar da shi, saboda haka kayi kokari da farko ka karfafa iradarka ka lakantawa kanka da cewa babu wata damuwa  zuciyarka ta samu nutsuwa bayan da ta kasance cikin raurawa sannan ka lazimci karanta kur’ani  da kuma yin wasu zikirai daga azkaru musammam ma salatuttuka da istigfarida tasbihohi guda hudu, lallai suna kawar da yawaice-yawaicen damuwa ga barinka da barin zuciyarka, ku saurara da ambaton Allah zukata suke samun nutsuwa ruhi ke nutsuwa damuwa ta kau a fara da sabuwa rayuwa mai cike da farin ciki  tacewa da da`da`da su jagoranceta insha Allah ta’ala    

        Allah ne abin neman taimako

 

Tarihi: [2017/11/11]     Ziyara: [4153]

Tura tambaya