mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Duk wanda bai da malamin tarbiyya cikin sairi da suluki me zai yi kenan?

Duk wanda bai da malamin tarbiyya cikin sairi da suluki me zai yi kenan?

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

بسم الله الرحمن الرحيم

Sai ya fuskanci Allah yana tsarkake da tsarkake kansa ya roki Allah kan ya zame masa malamin tarbiyya.

Ya zo cikin hadisin manzon Allah (s.a.w)

قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم أدبني ربي فأحسن تأديبي وأنا أدبت علياً عليه السلام وعلي أدّب شيعته

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ubangijina ya mini ladabi sai ya kyawunta ladabtar dani ni kuma na yiwa ali ladabi amincin Allah ya kara tabbata gareshi shi kuma ali ya ladabtar da shi’arsa.          Saboda haka ka nema daga Allah shi da kansa ya zama malaminka da farko sannan manzon Allah (s.a.w) sannan sarkin muminai ali (as). Duk wanda ma’asumi ya kasance mai masa tarbiyya lallai shi ba zai dinga kuskure ba cikin tafiyarsa da sulukinsa sabanin wanda mai masa tarbiyya ya kasance koma bayan ma’asumi ta yiwu ya karkacewa hanyar gaskiya da tafarki madaidaici.

Allah ne abin neman taimako 

Tarihi: [2017/11/10]     Ziyara: [780]

Tura tambaya