mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Mene ne ingancin maganar cewa matayen Imam Husaini (a.s) sun cire hijabi bayan kisansa

Salam Aaikum.
Ina neman Amsa daga hallararku kan tambayoyina shine cewa ya zo cikin ba’arin litattafan shi’a alal misali cikin littafin Irshad na Shaik Mufid da littafin Muntahal Amal na Shaik Abbas Qummi cewa an kwabewa matan Imam Husaini (a.s) Hijabi bayan shahadarsa, sannan shin ya inganta cewa gashinsu ya bayyana a fili??
Allah ya saka muku da alheri ya kuma tsawaita rayuwarku albarkacin Husaini shahidi (a.s)

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya kasance a zamanin A’imma mata hashimawa suna rufe jikinsu da hijabi da kyalle uku kyalle nikabi wanda suke lullube fuskarsu da sai kuma kyallen da suke lullube kirjinsu zuwa cibiya, sai kyalle na uku da suke rufe baki dayan jikinsu da shi kamar misalin abaya a zamaninmu, a binda ake nufi da an kwabe musu hijabi shine an cire  musu abaya ma’ana kyalle na uku sannan gashinsu bai bayyana a fili ba, kadai dai sun kasance sun kwance gashinsu sannan shi kwance gashi a wajen larabawa bai nufin fito da shi fili a’a abinda ake nufi shine kwance kitso sakamakon larabawa idan suna cikin farin ciki sukan kulle gashinsu da kitso  idna suka shiga halin damuwa da bakin ciki sai su kwance shi don ya zama alama da yake nuni da bakin ciki da suke ciki, wannan hsine abinda matayen hashimawa sukai a ranar Ashura lallai sun kwance gashinsu cikin hemomi yayin da mafi girman musiba ta sauka kansu wato kisan Husaini (a.s) da iyalansa da sahabbansa, sai suka kama dukan fuskarsu da kirajensu saboda tsananin bakin ciki, wannan shine misalin abin da na gani daga gwaggona lokacin mutuwar kakana Allah ya jikan rai Sayyid Husaini  lallai naga `yan’uwan babata sun zauna sun kwankwance gashinsu ya mike tsaye sun doddokin fusakensu da kirajensu, har yanzu ina tunawa da wannan lokaci a lokacin inada shekaru goma da haihuwa na ji matukar bakin ciki da radadi na yi ta zubar da hawaye na kuma tuna da kakata Zainab Haura (a.s) da wadanda suke kewaye da ita gindin jana’izar Imam Husaini (a.s) suna masu kuka suna kwance gashinsu suna dukan kirjinsu, la haula wala kuwwata illa billah, da sannu wadanda sukai zalunci zasu san wacce majuya zasu juya kyakkyawar makoma tana ga masu tsoran Allah

 

Tarihi: [2018/12/24]     Ziyara: [682]

Tura tambaya