mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

MAI BARIN SALLAH


Mutumin da bai yin sallah matsaloli ke ta samunsa daga kowanne tudu da ganage sai kuma wai yake cewa lallai idanuwan mahassada suke kansa tare da cewa yana da komai da komai daga tarkacen duniya.



Mutumin da bai yin sallah matsaloli ke ta samunsa daga kowanne tudu da ganage sai kuma wai yake cewa lallai idanuwan mahassada suke kansa tare da cewa yana da komai da komai daga tarkacen duniya.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin wanda baya yin sallah hakika ya kafircewa ni’imomin Allah matsarkaki sannan dukkanin wand aya kafirce lallai azabar Allah tanada radadi cikin gidan duniya da lahira , idan kuma kuka gode sannan ita sallah tana daga nuna godiya kan ni’imomin Allah lallai Allah zai kara ni’imar.

 (لَئِنْ شَكَرْتُمْ لأَزِيدَنَّكُمْ وَلَئِنْ كَفَرْتُمْ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٌ).

Lallai idan kuka gode tabbas zan kara muku lallai kuma idna kuka kafirce lallai azaba ta na da radadi.

Me yafi kyawu daga mutum idan akai masa kyautar da wata kyauta kamar misalign wata flower ace ya nuna godiya ga wand aya bashi wannan kyauta da harshensa lallai shi idan bai nuna godiya ba ma’abota hankula za su danganta masa munana ladabi da yin jafa’i da rashin nuna mutumtaka bari dai za su ganshi kasa da dabbobo bari dai mafi bata daga dabbobi, saboda kare ma idan akai masa kyautar kashi lallai ya na nuna godiya ta hanyar karkada jelarsa, to yaya mutum lallai Allah yayi masa kyauta ni’imomi wadanda basi kidaituwa basa kuma iyankantuwa ya isar masa babban misali lafiyar idanuwansa wadanda da su ne yake gani, idan kuma wani ciwo ya same shi sai ka same shi yana bayar da kudade masu yawa domin samun lafiyarsu gas hi ya same su lafiyau lau da ludufin Allah ta yay aba zai godewa ni’imar Allah da wannan ni’imar ido da ya ba shi ba, yana daga cikin jafa’ai da dabbanci ace bawa bai godewa ubangijinsa, sannan ita sallah itace mafi girman alamar godiya ga Allah matsarkaki, lallai idan  muka tambayi Allah yaya za mu godewa ni’imominka masu girma wadanda basu kidaituwa basu iyakantuwa lallai zai ce:    

 (أقيموا الصلاة لذكري)

ku tsayar da sallah domin gode mini domin in bude muku kofofin arzikina cikin duniya da lahira ku kasance cikin masu farin ciki da azurtuwa.

(أما الذين سعدوا ففي الجنة هم فيها خالدون)

Amma wadanda suka azurtu lallai suna cikin aljanna suna halin dawwama cikinta.

Ashe Imam Husaini wanda raina yake fansarsa bai kasance cikin tsakiyar yaki ba cikin tsakiyar ruwan kibbai da masuna suna zakke masa daga dukkanin tudu da ganagare sai dai cewa shit tareda haka ya tsaya a filin Karbala ya tsayar da sallah tareda yan tsirarun sahabbansa, shin anya kuwa mu Shi’ar Husaini ne ko kuma dai Shi’ar Abu Sufyan bari dai hatta shi’ar Yazidu sun kasance suna yin sallah sai dai cewa sallarsa ta kasance ba tare da Imami ba sai sallar ta kasance gurbatacciya sai dai cewa kai dan shi’ar Husaini ne ta yaya za a ce baka sallah mene ne ya kekasantar da zukatanmu me yafi batanmu me yafi jahilcinmu yawa, lallai kowacce rana Ashura ce kowacce kasa ma karbala ce kowacce rana rana ce ta yin sallah, sallah amudin addini ce idan ta karbu sauran ayyuka sun karbu idan akai wurgi da ita sauran ayyuka ma babu labarinsu. Sannnan hem aba tareda amudi ban a nufin rushewa da azaba da tsiyata da mummunan karshe Allah ya tsare mu.

Ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah cikin sallarku lallai ita amudin addininku ce wasiyyar ubangijinku ce da Imamikn zamaninku.

Allah ne abin neman taimako.

 الله الله بصلاتكم فإنها عمود دينكم ووصيه ربكم ونبيكم وإمام زمانكم والله المستعان.

 

Tarihi: [2018/4/16]     Ziyara: [4147]

Tura tambaya