b Shin zai iya yiwuwa ayi suluki zuwa ga Allah a kauda hijaban duhu ba tare da tallafin cikakken malami ba?
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin zai iya yiwuwa ayi suluki zuwa ga Allah a kauda hijaban duhu ba tare da tallafin cikakken malami ba?

Shin suluki zuwa ga Allah da yaye hijaban duhu zai yiwu ba tare da tallafin cikakken ustazu ba?
Shin a wannan zamanin namu akwai irin wadannan malaman cikin wannan fage a cikin hauzatul ilimiyya mai tsarki shin zai yiwu yayi darasin sairi da suluki zuwa ga Allah?

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai

Ta fuskanin imkani na zati eh zai iya yiwuwa sai dai cewa akwai magana cikin yiwuwarsa ta afkuwa tabbas ya zo cikin hadisi cewa

(هلك من لم يكن له حكيم يرشده)

Ya halaka duk wanda bai da malamin da yake nusantar da shi.

Daga cikin manyan malamai akwai wanda ya fassara wannan magana da ma’anar ustazunka cikin tafiyarka da sulukinka cikin kowanne ilimi daban, lallai yadda lamarin yake kamar yadda muke da bukatuwa da ustazu cikin fikihu da usul da ilimummukan da ake dauka a makaranta haka muke da bukatuwa da shi cikin irfani, ita kasa bata taba wofinta daga barin hujja daga barin ustazu cikin akhlak da irfani  kadai abin da yahau kanka shi ne ka nema ka bincika ustazu ka kwankwasa kofofinsu tareda naci da kafewa, lallai yadda lamarin yake duk wanda ya kwankwasa kofa ya matsa zai shiga, duk wanda ya dage zai samu

Allah ne abin neman taimako    

Tarihi: [2017/11/10]     Ziyara: [829]

Tura tambaya