mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Menene magani da mafita daga rashin samun aikin yi da rashin karbuwa wajen mutane tare da cewa ni lazimci wasu ayyukan ibanda na mustahabbi cikin neman arziki kamar misalign neman arziki


Salamu alaikum sayyid mai girma
Menene mafita kan rashin aikin yi da rashin karbuwa wajen mutane da toshewar arziki tare da cewa ni din nan na lazimci wasu ayyukan ibada na mustahabbi wajen neman arziki misalin sallar neman arziki wacce hallararku kuka ambaceta daga annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata gareshi da iyalansa tsarkaka da kuma azkaru masu yawan gaske da riwayoyi wadanda duk na karantasu daga littafai da aka rawaito su daga ahlil-baiti (as) amma tareda haka yanayin yana nan yadda yake a baya babu abinda ya cnaja ko ya sauya bari ma dai kullum sai kara tabarbarewa yake yi ban samu waraka ba da mafita har zuwa yanzu kamar yadda na baku labara a baya lallai inada yawan aiki da binda ya zo cikin littafin mafatihul jinan da makarimul akhlak da wasunsu sai dai babu wani ciagaba da aka samu ku nusantar da mu zuwa ga abinda cikinsa mafitar take. Allah ya baku lada ya kuma saka muku da alheri.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hadisi mai daraja ya zo daga imam rida (as) daga Allah madaukaki matsarkaki

 (احسن الظن بالله، فان الله عزّوجّل يقول: انا عند ظن عبدي المؤمن بي ان خيراً فخيراً و ان شراً فشراً)

Ka kyautata zato ga Allah* tabbas Allah mai girma da daukaka yana cewa: lallai ni ina nan inda bawana mumini ke zatona idan alheri yake zato sai ya same shi idan sharri yake zato sai ya same shi.

Haka ma an karbo daga imam (as) ya ce:

:«وجدنا في كتاب عليّ‌بن‌ابي‌طالب -عليه‌السلام- انّ رسول الله -صلی الله‌ عليه‌ وآله‌ وسلم- قال و هو علی منبره: و الله الذي لا اله الاّ هو ،ما اعطي مؤمن خير الدّنيا و الاخرة الاّ بحسن ظنّه بالله و رجائه، و حسن خلقه، و الكفّ عن اغتياب المؤمنين.و الله الذي لا اله الاّ هو لا يعذّب الله مؤمناً بعد التّوبة و الاستغفار الاّ بسوء ظنّه بالله و تقصير من رجائه بالله، و سوء خلقه، و اغتيابه للمؤمنين.و الله الذي لا اله الاّ هو لا يحسن ظنّ عبد مؤمن بالله الاّ كان الله عند ظنّ عبده المؤمن به، لانّ الله كريم بيده الخيرات، يستحي ان يكون عبده المؤمن قد أحسن به الظّن و الرّجاء ثمّ يخلف ظنّه و رجاءه له، فاحسنوا بالله الظّنّ و ارغبوا اليه»

Mun samu cikin littafin Ali bn abu dalib (as) cewa manzon Allah tsira damincin Allah ya kara tabbata gareshi da iyalansa- halin yana kan mimbarinsa yace: na rantse da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, ba abaiwa mumini alherin duniya da lahira ba sai don kyautata zatonsa ga Allah da kuma fatansa, da kyawun halayensa da kamewa ga barin gulma da cin naman muminai, na rantse da Allah wanda babu abin bauatawa da gaskiya sai shi babu wani bawa mumini da zai kyawunta zato ga Allah face Allah ya kasance wajen zatonsa. Saboda shi mai karamci ne a hannunsa alherai suke, Allah yana jin kunya ace bawansa mumini ya kyautata zato da fata gareshi sannan ya saba ma zatonsa da fatan da ya yi masa, ku kyawunta zato ga Allah ku yi kwadayi zuwa gareshi.

Sannan fadinka cewa yanayin yana ta kara munana shin wannan yana daga kyautata zato ga Allah shin yana daga kyautata zato ga ayyukan mustahabbi da azkaru, ya zama wajibi ka karfafa tauhidinka cikin zuciyarya ka dinga kokarin karanta suratu tauhid cikin kowacce rana sau dari  tareda lura da tunani  ba gundarin mommotsa harshe ba hatta kar ya zamanto baka ganin tasirinta  cikin samuwarka da rayuwarka, aibinfa daga garemu yake bawai daga Allah ba bawai daga zikiran ba da ayyukan mustahabbai, saboda ka duba tawaya cikin tauhidinka  cikin samuwarka.

                                                        Allah ne abin neman taimako

Tarihi: [2017/11/7]     Ziyara: [796]

Tura tambaya