b Shin yin kuka cikin mafarki alama ce ta bala’ai da mummunan karshe?
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin yin kuka cikin mafarki alama ce ta bala’ai da mummunan karshe?

Ni uwa ce da na rasa `dana wanda shekerunsa sun kai 25 to shine a wani dare a mafarki na ganshi kamar mara lafiya cikin wani akwatu na katako lokacin da aka dawo mini da ruhina san nace zan kara ganinsa sai kawai na dinga kuka sai nace masa ya dana in baka raina sai yace: a a ya umma da kinsan wahalar hakan da baki aikata ba sai dai cewa ki bani rabin ranki daga karshe sai na ganshi a wajen akwatun kansa na cikin dakina ni kuma ina tayi masa kuka.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Kuka alama ce ta farin ciki insha Allah zaki ji jarrabawa ce mai kyau zai shigar da farin ciki cikin zuciyarki insha Allah, daga karshe ina rokon Allah  yaye miki bakin ciki da damuwa ya kuma azurta  da hakuri da wankewar zuciya daga bakin ciki.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2018/2/6]     Ziyara: [870]

Tura tambaya