Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
ko da yaushe ina bakin kokarina wajen ganin na nesantu daga aikata zunubai domin ibadata ta karbu
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

ko da yaushe ina bakin kokarina wajen ganin na nesantu daga aikata zunubai domin ibadata ta karbu

Salam Alaikum
Hakika koda yaushe ina bakin iyawata cikin kauracewa zunubi domin in kebantu da wani daga karbuwa bakin kofar ubangijina lokacin tsayuwata gabansa, sai dai cewa ni matsalata shine saurin fusata na rasa yanda zanyi in rabu da wannan al’ada kowanne lokaci wannan al’ada tana hana ni cimma burina.

Allah shi kareka Sayyid daga dukkanin mugun abu, daga karshe ina fatan kai mini nasiha da wata mafita daga wannan matsala, lallai nema maka alkawarin addu’a wurin ubangijina lallai shi mai yawan kyauta ne mai kuma karamci ne.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya kai wannan bawan Allah hakika (samu yana daga cikin sunayen mutuwa kuma daga sammu ya samo asali) amincin Allah ya tabbata gareka   

 (إن الشيطان عدو لكم فأتخذوه عدواً)

Lallai shaidan makiyinku ne kuma ku rike shi makiyi

Wannan shine abin da ubangijin talikai ya fadi cikin littafinsa tsarkakakke, na’am misalin wannan shaidani makiyi mai tsananta kiyayya baya kyale mutum ya huta bari dai yana jefa shi cikin gafala da biyewa sha’awe-sha’awe da aikata zunubai sai dia cewa wajibi ka yake shi ta hanyar watsi da aikata kaba’ir amma kananan zunubai lallai Allah yana kankare su ya sauya su da kyawawa ya kuma gyara halin da bawansa yake ciki.

 (ان يجتنبون كبائر ما تنهون عنه نكفّر عنكم سيئاتكم وندخلكم مُدخلاً كريماً) (النساء: 31).

Idan kuka kauracewa manyan laifuka daga abinda aka haneku zamu kankare muku munanan ayyukanku kuma mu shigar da ku mashigar karamci

Amma shi fushi to ya kamata ka lazimci ambaton sunayen Allah musammam ma (ya halimu) kamar yanda na rubuta littafi kan maudu’in (fushi da hakuri) an buga shi kuma zaka iya samunsa a sayit dinmu na (Alawy.net) bangaren litattafai

Allah ne mai taimako.

Tarihi: [2018/12/15]     Ziyara: [621]

Tura tambaya