mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Hukuncin istimna’i (yin wasa da al’aura) lokacin larura ga mata

Nayi aure ina da shekaru sha takwas da haihuwa amma banajin `dadin ala`kar jima’i da mijina, sannan shi mijina bai da wayewar yin romance (wasa da juna gabanin jima’i) wanda hakan ta kai ni ga komawa ga yin wasa da al’aura ta saboda
tsananin bukata shin aikata hakan da
nayi ya zama sabo

 


?  

بسم الله الرحمن الرحيم

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Istimna’i (wasa da al’aura) ya haramtu mudlakan kuma yinsa sa`bo da yake jawo azaba da ukuba ranar alkiyama matukar dai mai aikatawar bata tuba ba ta yi watsi da zunubi, kiyi kokari cikin yiwa mijiki bayani halin da kike samun kanki ciki tabbas wasa da juna mustahabbi ne gabanin yin jima’i: da farko a fara da musayen kalaman da suke motsa sha’awa tsakanin juna da kuma amfani harshe sai kuma wasa da juna, kowanne mai aure akwai tsarin da yake da shi cikin hakan a kebance sannan bayan haka sai a tsallaka zuwa ga rungume juna sai kuma kusantar juna (jima’i) hakika na kawo wasu adadin bayanai daga cikinsu cikin littafi na mai suna (zahrul rabi’u) cikin karshensa akwai abubuwa da zasu amfanar cikin wannan babi.

Sannan ita wannan garizar ba ta daga tsarin halittar Allah da ya halicci mutane a kai wacce ta ke son kamala tsantsa da kyawu tsantsa bari ita dai gariza ce ta jinsin dabbanci wacce daga cikin hikimar ta shi ne wanzuwar nau’in mutum ko kuma dabba, kamar yadda daga cikin hikamar ta cigaban dangantakar ma’aurata cikin alakarsu ta auratayya da dangi lallai shi jima’i wani jigo ne babba muhimmi ciki wanzuwar `kauna  da soyayya tsakankanin ma’aurata sannan kuma shi ya kasance mafi da`da`dar da`di kamar yadda ya zo cikin hadisi daga ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata gare su da kuma yawan saduwa da mata yana daga sunnonin annabawa (as) yayinda muke dandakakken bincike kan saki aure zamu gano tushensa ya samo asali ne daga rashin jin da`din juna ga ma’aurata lokacin kunsantar junansu ta aure.

Sannan dama shi lamarin yadda yake dukkanin wani mumini da mumina ana jarraba su cikin rayuwarsu da wata jarrabawa daga Allah don jarraba su domin ki sani shin ke kina daga ahalin masu tsoran Allah da wutar jahannama ko kuma son zuciyarki da tsiyarki ke galaba kanki kike aikata haram.

Saboda haka ki ji tsoran Allah hakikanin tsoransa kada ki kara kusantar kwatankwacin wannan aiki da mummunan zunubi ki sallamawa hukuncin Allah da kaddararsa, lallai haka Allah ya kaddara miki miji wanda bai fahimtar hakikanin mace da bukatunta da sha’awarta lallai ita mace tana da sha’awa goma shi kuma namiji an bashi guda daya daga ciki, idan ya zamanto bai kosarta da ita lokacin jima’i lallai ita za ta kasance kasansa tana burin kasancewa tare da mafi munin mutane domin ita sha’awa wani abu ne daban kyawu da dukiya wani abu daban.

Muna rokon Allah ya baiwa maza fuskanta da ilimi domin su san hakikanin mace daga dukkanin bangarorinta da sha’aninta, kamar yadda muke rokonsa da ya ba da fahimta da ilimi ga mata da kuma kamewa da hakuri da jin kunya domin su samu damar sanin namiji da hakikaninsa, ina rokon Allah ya gyara lamarinki cikin gaggawa ba tareda jinkiri ba, ya zama wajibi ka rungumi tsoran Allah ki rike tsoran Allah da tsantseni da taka tsantsan, da tsoran azabar Allah da haduwa da shi. Amma dukkani wanda ya ji tsaoran tsayuwa da ubangijinsa ya hana zuciyarsa abin da take so daga sha’awa da istimna’i  lallai aljanna ita ce makomarsa matsuguninsa da izinin Allah madaukaki.

Allah ne abin neman taimako dukkanin godiya ta tabbata ga Allah karshen kiranmu godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talika

  


 

Tarihi: [2017/11/1]     Ziyara: [55939]

Tura tambaya