mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin rashin Imani na da Wilaya Takwiniyya yana iya fitar da ni daga Mazhaba?

Salamu Alaikum Assayid abin girmamawa gareni, hakika ni `dan Shi’a ne sai dai cewa tareda haka ban yi Imani da Wilaya Takwiniyya ba kuma ban yarda da karamomi da mu’ujizozin Annabawa da A’imma (a.s) ba, shin wannan rashin imanin nawa da rashin yarda zai iya fitar da ni daga cikin shi’anci?

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Hakika Wilaya Takwiniyya mu’ujiza ce da karamomi lallai tana daga kyautar ubangiji ga bayinsa karramammu wadanda basa gabatarsa da zance, lallai wilayarsu tana kewaya ne cikin wilayar Allah, bas aikata wani aiki cikin wilayarsu sai dai izinin Allah matsarkaki, wannan wani abu ne da dukkanin musulmai suka yi Imani da shi tareda sassabawar mazhabarsu, sai dia cewa a cikin Mazhabar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu, mun yi Imani da cewa wannan kyauta ta ubangiji ya bada ita ga A’imma bari ma dai ya bada ita hatta ga ba’arin wasu daga cikin shi’arsu, sai dai cewa su wilayarsu juzu’iyya ce iya cikin ba’arin wasu muhallai kebantattu, amma wilayar Annabawa da Wasiyyai kulliya ce sakakkiya , hakika na wallafa littafi kan haka cikin wilaya takwiniyya da tashri’iyya cikin bayani filla-filla.

Allah ya dawwamar daku cikin alheri.

Tarihi: [2020/6/11]     Ziyara: [455]

Tura tambaya