mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ko zaku iya tabbatar mana da ma’asumancin Annabi Adam (as) ta hanyar Saklaini Da sunan Allah mai rahama mai jin kai Manzon Allah (s.a.w) yace

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Manzon Allah (s.a.w) yace:

إني تارك فيكم الثقلين ما إن تمسكتم بهما لن تضلوا: كتاب الله، وعترتي أهل بيتي

Lallai ni ina bar muku nauyaya guda biyu matukar kuka yi riko da sub a zaku taba bata a bayana ba: littafin Allah da zuriyata mutanen gidana.


  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Manzon Allah (s.a.w) yace:

إني تارك فيكم الثقلين ما إن تمسكتم بهما لن تضلوا: كتاب الله، وعترتي أهل بيتي

Lallai ni ina bar muku nauyaya guda biyu matukar kuka yi riko da sub a zaku taba bata a bayana ba: littafin Allah da zuriyata mutanen gidana.

 

Salamu Alaikum ina gaisuwa ta Imani gareku, Allah matsarkakin sarki ya bamu labara cikin littafinsa karkashin aya mai albarka kan sabon da baban Annabawa Adam ya aikata, haka ma A’imma (as) sun labarta mana sunyi ishara zuwa ga sabaon da ya aikata daga cikin akwai fadin Imam Ali (as) (sai ya sayar da yakininsa da shakkarsa azamarsa da rauninsa…..sannan Allah ya shimfida masa cikin tubansa) sannan  Imam Sajjad (as) yana cewa:

"وَالْمُنِيبُ الَّذِي لَمْ يُصِرَّ عَلَى مَعْصِيَتِكَ، وَسآبِقُ الْمُتَذَلِّلِينَ بِحَلْقِ رَأْسِهِ فِي حَرَمِكَ، وَالْمُتَوَسِّلُ بَعْدَ الْمَعْصِيَةِ بِالطَّاعَةِ إلى عَفْوِك

Kuma da tubabben da bai kafe kan sabonka ba, kuma magabacin masu Kankan da kai da saisaye gashin kansu cikin haraminka, mai kamun kafa da `da bayan aikata sabo da afuwarka.

 

1-ku tabbatar mana ismar Adam (as) da kur’ani da hadisi

2-shin kun yarda da isma zamaniya da makaniya?

Idan har baku amsa wannan tambayoyi ba, ba zaku taba iya amsawa ba. To fa ku sani akidar ismar annabawa akida ce daga makarantar Ahlus-sunna da wasu daga shi’a suka kwaso ta daga can suka kawata suka shigar mana da ita cikin tunani da akidu, suka kiraye da dunan isma mudlaka da gairu mudlaka, duk mutum mai bibiyar ra’ayoyi da nazariyoyin malaman shi’a zai samu wannan batun cikin raurawa da rashin tsayayyiyar Magana.

 

Naku Abdul-Wahab.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Wannan jiji da kai naka haka har ina?! Kana hakaito ra’ayoyin wasu mutane kamar tsutsun Ak, kana wani cika baki da cewa waio idan baku amsa ba zaku amsa ba har abada, shin baka tsammani lokaicn bayyanar Imamul Hujja (as) zai bada amsa kan ismarsa kuma shi maganarsa rarrabewa ce, ko kuma dai kaima kana da matsala da ismarsa ta yanda da hakan zaka fice daga da’irar Mazhabar shi’a imamiya?! Lallai mai bibiyar ra’ayoyin malaman shi’a ba zai same cikin raurawa ba, bari dai kake raurawar kwakwalwa matukar raurawa, don me kake hukunci kan mai bibiya ba tareda izininsa ba, lallai wannan zalunci ne da ta’addanci kan `yancin ra’ayi , tama yiwu mai bibiyar yafi ka sani ya kuma gamsu da ra’ayoyin shi’a kuma ya kasance mai sallamawa ba mai tsaurin kai ba, domin shi mai kin gaskiya da tsaurin ko da zaka zo masa da dalili dubu ba zai taba karba daga gareka kamar yanda ya kasance cikin kissar Zamakshari da Mishkini da dalibansa, shi mai kin gaskiya kamar mutum da yake barci da gangan alhalin a hakika ba barci yake ba, lallai ko da zaka kira shi sau dubu lallai ba zai amsa maka ba, amma idan ya kasance a hakika baccin yake kuma hakika ya jahilci mas’alar bai santa ba, to lallai kira na farko ko na biyu zai amsa maka ya farka daga baccin da yake, saboda haka ka binciki kanka kan wadannan furuci da hukunci kan mai bibiya da kwace masa `yancinsa da ka yi, lallai hakan na daga tsaurin kai, ka duba sosai ka gani shin kuwa baka sa matsalar raurawar kwakwalwa kuwa?!

Lallai idan kayi riko da maganganun malaman mazhabar Ahlil-baiti lallai zaka samu sun fassara sabon Adam da ma’anar barin ya kamata, ka duba Tafsirin Burhan da Tafsirin Saklaini da Mizan da Amsal karkashin bayanin wannan aya mai albarka da ta kunshi kissar cin dan itaciyar bishiyar da aka hana shi kusantar ta, lallai zaka san cewa iliminka bai wuce cikin cokali ba abubuwa da baka sani ba sun haura wanda ka sani.

Sannan ka riki hadisi guda na sarkin muminai (as) ka yi watsi da gomomin hadisai da suke tsarkake Adamu (as) daga aikata sabo, lallai ka sani cewa maganar sarkin muminai (as) tanada irin harshenta da ma’anarta kebantacciya, idna wannan hadisi guda ya kasance yana cin karo da gomomin riwayoyi da suke nuni kan ismanci Adamu (as) to a irin wannan lokaci dole a tattarasu ayi tawilin maganar, wannan hukunci na gudana cikin zahirin nakali idan suka zamanto suna sabawa hankali, alal misali fadinsa madaukaki:    

 (يد الله فوق أيديهم)

Hannun Allah yana saman hannayensu.

Wahabiyawa sun riki zahirin ayar sai suka ce lallai Allah yanada hannu sai ba irin hannayen mutane ba, sai dai cewa wannan yana sabawa da dalilin hankali na cewa Allah bai da jiki domin idan ya kasance yana da jiki zai lazimta masa jerantuwa da bukatuwa wanda hakan na daga siffofin mumkini shi kuma Allah wajibul wujud ne ga zatinsa, ya zama dole ayi tawili hannu da cewa abin nufi da hannu ikonsa bawai cewa Allah yanada gabar hannu ba, haka al’amarin yake ciki sabon Adamu hakan yana da cin karo da dalilin hankali, domin cewa a hankalce dole ne annabi ya kasance katangagge daga sabo, sabanin haka zai zama fadin Allah kju bishi saki babu kaidi tareda kuma cewa yana iya aikata kuskure da sabo hakan zai lazimta komar da jahili zuwa ga jahili wanda hakan abu ne mai muni a hankalce, saboda haka dole ne mu tafi kan ismar Adam (as) mu fassara sabonsa da ma’anar barin ya kamata don gudun kada a samu cin karo da ismarsa, wannan ba ijtihadi bane kishiyar nassi, bari ijtihadi ne cikin tafsiri da bayanin nassi.

Allah mai datarwa da yin damdagatar.

Tarihi: [2019/3/16]     Ziyara: [721]

Tura tambaya