mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Menene ayyukan da suka wajabta akan mujtahidi a zamanin gaiba kubra, menene banbanci tsakanin na’ibin imam da wakilin imam shin kun tafi kan na’ibanci da wikalanci?

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.
Sayyid mai daraja da girma ina da wasu `yan tambayoyi wanda sune kamar haka:
Tambaya ta farko: menene wajibin mujtahidi a lokacin gaiba kubra?
Tambaya ta biyu: menene banbanci tsakanin na’ibi da wakili ga imam (as) ?
Tambaya ta uku: shin kuma kun tafi kan na’ibanci da wakilanci

Menene ayyukan da suka wajabta akan mujtahidi a zamanin gaiba kubra, menene banbanci  tsakanin na’ibin imam da wakilin imam shin kun tafi kan na’ibanci da wikalanci?

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Sayyid mai daraja da girma ina da wasu `yan tambayoyi wanda sune kamar haka:

Tambaya ta farko: menene wajibin mujtahidi a lokacin gaiba kubra?

Tambaya ta biyu: menene banbanci tsakanin na’ibi da wakili ga imam (as) ?

Tambaya ta uku: shin kuma kun tafi kan na’ibanci da wakilanci?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Wa alaikum salam warahmatullah

Wajiban mujtahidi a zamanin gaiba kubra misalin kowanne ya yada hukunce-hukuncen addini yayi hidima ga shari’ar manzanni (as) dukkaninku makiyaya ne kuma dukkaninku ababen tambaya ne kan abinda aka baku kiwo, sai dai cewa kowanne mutum guda yana daukar nauyin da ya hau kansa ne gwargwadon yanayin yadda zai iya da zarfiyyarsa, daga wajibin da yake kan mujtahidi shi ne ya shiryar da mutane zuwa hanya mikakka ya kuma sanya ijtihadinsa cikin hidimtawa shugabanmu sahibuz zaman (as) amma na’ibanci da wakilci to su biyun kalmomi ne mutaradifai da suke da ma’ana kwaya daya dangane ga wanda ya dangane zuwa ga sahibul amr (as) kadai itace na’ibance gamamme da wakilci gamamme ba tareda bayani `baro-`baro ba daga imam (as) bari da zance gamamme  da ya zo daga ahlul-baiti amincin Allah ya tabbata garesu kamar mnisalin fadinsu:

 (من کان من الفقهاء ... فرجعوا الیهم )

Wanda ya kasance daga fakihai…. Ko koma zuwa garesu.

Wakilci da na’ibanci bas u ksance kebance ba, duk kuma wanda yake da’awar cewa shi yana ganin imam Mahdi (as) wai kuma imam din ya bashi wakilci da na’ibanci tabbas katon makaryaci ne makagi tsinuwar Allah matsarkaki da tsinuwar imam Mahdi (as) ta  tabbata kansa.

فمن ادعی الرؤیة فکذبوه.

Duk wanda yayi da’awar cewa ya ga imam mahadi ku karyata shi.

Tarihi: [2017/8/13]     Ziyara: [1013]

Tura tambaya