mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Yaya zaku martini kan shehin wahabiyawa adnan ar’ur da irin cin mutuncin da yake muku ko kuma dai abin da yake fada gaskiya ne kanku mazhabar taku baki dayanta karya ce?

Yaya zaku martini kan shehin wahabiyawa adnan ar’ur da irin cin mutuncin da yake muku ko kuma dai abin da yake fada gaskiya ne kanku mazhabar taku baki dayanta karya ce?

Shin zakuyi martani kan adnan ar’ur da cin fuska da yake muku koko yana kan gaskiya mazhabarku ce karya baki dayanta?

 

Da sunan Allah mai rahama mai ji kai

Mazhabar da muke kai gaskiya ce dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai babu shakka ko kokwanto cikin hakan gawargwadon kiftawar ido lallai tabbas mazhabar da muke kai ita ce addinin sarkin muminai Ali (as) manzon Allah (s.aw) cikin hadisin da akai ijma’i da ittifaki kai daga shi’a da sunna yana cewa :

 ( علي مع الحق والحق مع علي واينما دار يدور )

Ali yana tare da gaskiya gaskiya tana tare da Ali duk inda ya juya tana juyawa tare da shi.

A wani wajen kuma manzon Allha (s.a.w) ya ce: 

 أَنَا مَدِينَةُ الْعِلْمِ وَعَلِيٌّ بَابُهَا ، فَمَنْ أَرَادَ الْعِلْمَ فَلْيَأْتِهِ مِنْ بَابِهِ

Ni birnin ilimi ne Ali kuma kofarsa duk wanda yake son ilimi to ya zo masa ta kofarsa.

Kamar yadda matsarkaki madaukaki yake cewa :

 (وَ اْتُوا الْبُیُوتَ مِنْ اَبْوابِها)

Ku jewa gidaje ta kofofinsu.

Mu muna kan kur’ani da sunnar manzon Allah (s.a.w) ta hanyar kofar Ali (as) ba ta kofar wane da wane ba muna godewa Allah kan wannan shiriya zargin me zargi bai damunmu amma adnan ar’ur da misalsalansa ba sa bakin komai face karnuka da suke ta haushi ayari kuma yana tafiyarsa, amma kumfa to tana tafiya a iska amma abin da yake amfanar da mutane sai ya wanzu a ban kasa, Allah matsarkaki madaukakin sarki yake bada kariya ga wadanda sukai imani. Tabbas hsi’anci yana ta yaduwa a sasanni duniya kamar yadda hasken rana ke yaduwa da fantsama dukkanin godiya ta tabbata ga Allah

 

Tarihi: [2017/11/7]     Ziyara: [776]

Tura tambaya