mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

INA SON KU YI MINI WASICCI DA WATA HANYA ZUWA GA IMAM MAHADI (AS)

Salamu Alaikum. Assayid mai albarka da yardar Allah zaku kasance cikin alheri da lafiya
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Sayyid yawancin lokuta ina shauki ga Allah ta’ala, ina son in ga na kai ga zuwa ga Imam Mahadi (af) sai dai cewa ban san me na aikata ba da al’amarin ya tsananta ya kuntata kaina, ina son inyi karaji da babbar sautin sai dia cewa ina jin kunya kada mutane su jini, sai na tsare kaina cikin radadin, wani lokaci na kan fitowa in je wurare masu nisa cikin sahara in kirayi Imamul Hujja (as) ina kuka in yi sallah a can sannan sai in dawo gida, shin zan samu wata nasiha daga gareku da nake fatan ta zama mafita cikakka mai warakarwa.

Nasihata shine ka tsarkake niyyarka, lallai duk wanda ya tsarkake niyya zai samu komai, da iklasi ne ake samun kubuta, baki dayan mutane halakakku ne face malamai, baki dayan malamai halakakku ne face masu aiki da iliminsu, masu aiki da iliminsu baki dayansu halakakku ne face masu tsarkake niyya, su kuma masu tsarkake niyya su kan hatsari, hakika riya tana tafiya tana gudana tana sadadawa kamar misalin tattakin bakar tururuwa cikin dare, wane ne zai ji karar tattakin ta. Allah ne mai bada taimako, babu tsimi babu dabara face da Allah madaukaki mai girma.

Tarihi: [2019/8/8]     Ziyara: [499]

Tura tambaya