b balagar yara maza
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

balagar yara maza

Ni shekarata goma sha uku gashin mara ya tsirar mini, sannan maniyyi ya fita daga gareni ta hanyar wasa da azzakari da nayi sai dai cewa gashin hammata bai tsiro mini ba sannan kuma ina mafarki shin na balaga kenan?

da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai
ana gane balaga ta hanya uku:
1-cika shekaru goma sha biyar
2-tsirar kausassan gashi a mara.
3- mafarki tareda fitar maniyyi.
saboda haka ka balaga sannan ka kauracewa aikata istimna'i da kayi hakika haramun ne kuma zai sanya ka shiga wuta da fushin Allah, kada ka fusata ubangijinka wanda ya baka dukkanin ni'ima, ka gode masa ta hanyar watsi da aikata haramun, sannan wajibi ne kan ka sauke wajibai, ina rokon ubangiji ya baka dacewa fa samun tdaftatacciyar rayuwa cike da farin ciki kuma ka kasance daga wadanda suke hidimtawa addini da mazhaba da mutane da Kasa, kada ka karar da kuruciyarka da makomar rayuwarka cikin shashanci, lallai zunubi yana zama sababin tsiyata da wahala duniya da lahira.
Ubangiji shine abin neman taimako
Tarihi: [2020/5/1]     Ziyara: [674]

Tura tambaya