mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

shin soyayyar Ahlil-baiti tana kasancewa daga bangare daya

shin soyayyar Ahlil-baiti tana kasancewa daga bangare daya
hakika ni ina son Alayen Annabi kuma ina son Imam Husaini amincin Allah ya tabbata a gareshi,
tambaya zuwa gareku shine shin yanzu ni na cancanci soyayyarsa shima zai so ni kena

hakika ni ina son Alayen Annabi kuma ina son Imam Husaini amincin Allah ya tabbata a gareshi,

tambaya zuwa gareku shine shin yanzu ni na cancanci soyayyarsa shima zai so ni kena.

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Ita soyayya wata alakac tsakanin masoyi da abin sonsa tana iya yiwuwa daga bangare daya kadai kuma tana iya kasancewa daga bangarori biyum sai dai cewa yana daga abinda akayi ittifaki aka sallama kansa cewa duk wanda ya so Ahlil-baiti tareda tsarkake niyya tabbas suma zasu so shi sabida duk wanda ya so wani mutum to lallai zai yi masa biyayya tabbas masoyi mai biyayya ne ga wanda yake so, duk wanda yake son Imam Hassan da Imam Husaini (A.S)  zai tsayar da sallah hatta cikin misalain ranar Ashura a kan lokacinta cikin jam’i yana mai tuba, duk wanda da gaske yana son Imam Husaini (A.S) lallai zai yi koyi da shi zai masa biyayya da `da’a zai tafi kan hanyarsa zai kasance yana sallah a kan lokaci kuma cikin masallaci cikin jam’i, duk wanda ya kasance haka to lallai shi Mumini ne mai tsoran ubangiji lallai Allah yana son masu takawa, kuma hakika A’imma suna son duk wanda yake son Allah, suna son masu takawa, idan ka kasance mai son su mai `da’a garesu mai takawa lallai babu shakka zasu so ka, amma kuma idan soyayyar tsuran wahami ne da hiyali da surutu kadai wanda baya lazimta soyayyarsu kamar yanda wani mutum ya gaya Imam Sadik (A.S) hakika ina sonka sai Imam ya dan sunkuyar da kai yace karya kake, sai mutum yace: ta kaka, sai Imam yace masa sabida hakika ni a zuciyata ban samu soyayyarka ba.

Wannan yana nuna cewa soyayya ta hakika da gaskiya tana kasancewa ne daga bangarori biyu tsakanin shi’a masu wilaya da kuma A’imma tsarkaka amincin Allah ya tabbata a garesu, hakika ana sanin gaskiya soyayya ta hanyar Imani da aiki nagari, duk wanda yake son Allah da Manzonsa da Ahlil-baiti babu makawa zai musu biyayya cikin kowanne abu cikin akidunsu da dabi’unsu da addininsu da hukunce-hukuncensu sai sallarsa ta kasance misalin sallarsu wannan cikin dukkanin ibada da mu’amala, kowanne mutum yana kan basira game da kankin kansa, shin kai kana da’a ga Allah da Manzonsa da Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu.
Tarihi: [2021/4/28]     Ziyara: [563]

Tura tambaya