mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

WANI LOKACIN INA SAMUN ZANTUKANKU CIKE DA ABABEN MAMAKI

Salam Alaikum.
Na kasance mai bibiyan laccocinku ni bana bin mazhabarku sai dai cewa tareda haka ni bani da ta’asubbancin mazhaba, kadai dai ina daukar kyakkyawa daga ko’ina, wasu ba’rin daga kyawawan sulukinku sun ja hankalina sai dai kuma sai na ci karo da yake warwara da suka kan Ahlil-baiti (a.s) sune tushen tawali’u jagoransu Sarkin muminai (a.s) sai dai cewa na sameku kuna danganta musu kiyayya da gaba da riko! Tun da dai su tsarkakakku kuma su kyawu ne bai kamata a danganta wani abu mara kyawu zuwa garesu, bama bukata wani tawile-tawile da wasu kawo ayoyi don malkwada ma’ana, matukar dais u tsarkaka kuma sune kofar sanun Allah to ba za a iya saninsu sai da tsarkakar zuciya tareda da dukkanin halittu da duk yanda suka kai.

Na samu wasu ba’arin zantukanku cike da akasin tsarkakar Ahlil-baiti na sha mamaki kan haka bai kama ace Arifi ya kasance da wannan tunani ba.

Allah ya datar da ku da mu baki daya dama dukkanin musulmi ya zuwa ga abinda yake so yake kuma yarda da shi ya kuma haskaka zukatanmu mu masu suluki kan hanyar gaskiya tareda tsarkake niyya.

 Wassalam

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Da farko Ina godiya kan kyautata zatonku kaina, sannan Magana ta biyu shine Allah ta’ala yana cewa: (kayi bushara ga bayina wadanda suke jin Magana suke bin mafi kyawunta) ta uku: barranta daga makiya bai cin karo da tawali’u bari ma dai shine ainahin tawali’u da Imani, domin kamalar Imani shine wilaya ga Allah da Manzonsa da gaskiya da Ahlil-baiti da barranta daga makiya Allah da makiya da makiya Manzon Allah (s.a.w) da Ahlil-baiti (as) da gaskiya, sannan ubangijin talikai shine kyawu tsantsa zatin siffofin rahama da jin kai lallai shi mafi jin kai masu jin kai, tareda haka kuma shine mai daukar fansa Almuntakimu  kamar yanda yake shine mafi tsananin masu ukuba cikin mahallin ukuba da azaba kamar yanda yake mai jin kai haka yake Almuntakimu shi daukar fansa da azaba suna daga siffa tsarkakar Allah siffa Jalaliya (ku siffantu da siffofin Allah) lallai daidai lokacin da zuciyar mumini take tsaftace haka take dauke da daukar fansa sai dai cewa kowanne yana kasancewa a muhallinsa.

Wannan maganar da kake ta cewa mu bama kafa hujja da aikin Allah wannan tsantsar jahilci ne da yake jawo kafirci ka ji tsoran Allah ka tuba saboda su kansu a’imma suna kafa hujja da kur’ani da littafin Allah da kum aikinsa, Imam Sadik (a.s) da kansa yana cewa ku dabi’antu da dabi’un Allah. Haka Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: ubangijina ya tarbiyantar dani ya kyawunta tarbiyatar da ni, saboda haka ya zama dole mu sallama kan mai gaskiya mu la’anci makiya wannan lamari ne da yake a bayyane da kuma kur’ani da ilimi saboda haka ne ma kake gani gomomin ayoyi sun zo da la’ana kamar la’antar azzalumai.  

Tarihi: [2019/9/16]     Ziyara: [623]

Tura tambaya