mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

MENENE YA SANYA ALLAH BAI KAFA WASU KA'IDODJI BA

salamu Alaikum

Samahatus Sayyid iana da wata tambaya hakika musulmai tareda dukkanin mazhabobinsu tun a farkon muslunc sun saba sabawa mai tsanani haka ma wannan zamani da muke ciki, kai hatta ta kai ga a cikin Mazhaba guda daya zaka samu sassabawa tsakanin `yan mazhabar har ta kai ga ba’arinsu suna kafirta ba’ari

Salamu Alaikum

Samahatus Sayyid iana da wata tambaya hakika musulmai tareda dukkanin mazhabobinsu tun a farkon muslunc sun saba sabawa mai tsanani haka ma wannan zamani da muke ciki, kai hatta ta kai ga a cikin Mazhaba guda daya zaka samu sassabawa tsakanin `yan mazhabar har ta kai ga ba’arinsu suna kafirta ba’ari ko fasikantar d aba’ari da nuna cewa yana kan bata da bidi’a, kai wani lokacin ma tana kaiwa ga su yaki junansu su zubar da jinin juna, idna muka bincika sababin da jawo wannan sabani da ya dora kan gaba da kiyayyar juna sai mu ga tushensa shine nassoshin shari’a kuma galibin nassoshi nassoshi ne na zanniyat da ba akai ga tabbatar da ingancinsu ko kuma wata dalalatu da take wurga mu cikin sabani da rudu, alal misali masu inkarin hujjiyar Kabarul wahid (hadisin da bai kai ga haddin tawatiri ba) da kuma masu tabbatar da shi dukkaninsu suna dalilai daga Kur’ani da ko kuma daga mutawatiran hadisai, haka zalika masu Imani kan yiwuwar ganin Imamul Hujja (as) suna da dalilan da suka ginu kai haka ma masu karyata ganinsa suna da nasu dalilan, akwai wasu mas’alolin Usul da Kalam ko na Fikhu kadai dai sabanin ya bubbuga daga garesu sakamakon nassoshin shari’a masu karo da juna sannan kowa yana da nasa dalilai daga littafin Allah ko daga hadisai kai hatta mas’alar imamanci idna muka bincika zamu samu cewa mazhabar shi’a cikin karnonin da su ka gabata kadai dai sun samu sabani cikin nassoshi ko dia sakamakon buyan nassoshin garesu ko kuma rashin yaduwarsu da rashin bayyanar ma’anarsu a fili a wurin wasu ba’ari ko kuma sakamakon cin karonsu da juna da sassabawarsu ko kuma sakamakon wasu dalilai na daban da suke haifar da shubuha da ishkali da tufka da warwara da sauran matsaloli da babu lokacin kawo a nan, bari dai akwai wasu ba’arin hadisai da suke nuni zuwa ga cewa A’imma (as) da gangan suka yada sabani da rarraba kawuna daga abinda yake gadar da shakku da rudu tsakanin `yan shi’a ta yiwu ma ya zama dalili da ya sanya wasu yan shi’a fita daga shi’anci kamar yanda Shaik Dusi yayi ishara zuwa gareshi a cikin mukaddimar littafinsa (Attahzib) abu mai muhimmanci shine cewa wannan sabani ya samu asali daga nassoshin shari’a da suke cin karo da juna, to ma ya sanya Allah bai sanya wasu ka’idoji bayyanannu da dokoki sannan me sanya bai saukar da nassoshi da zasu kasance a bayyane ba da zasu nesanta mu daga bin zato da tsammace-tsammace daga fuskar inganci isnadinsu da ma’anarsu kuma ya zama al’umma ta kasance cikin hadin kai da tsira daga fadawa cikin fitina da yaki da gaba da kiyayya, kuma ya zama al’amura basu shige musulmi cikin duhu da kaiwa ga sun fada cikin shakku da kauracewa gaskiya, ka’idojin da muke bukata ba wasu ka’idoji ne masu yawa kuma ai Allah yana da iko kan yin haka, shin ashe baya daga cikin hikima Allah ya aikata hakan ashe hakan baya daga ludufinsa da rahamarsa kan bayinsa, me ya sanya ya kyale mu a haka kan zato da tsammace-tsammace da suke gadar mana shakku ya kuma sanya nassoshinsa ma’anarsu bata fito fili ba,

Ina neman gafarar Allah ina kuma tuba zuwa gareshi, ina rikonsa shiriya da damdagatar.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hakika sabani da sassabawa abu ne mara dadi sai dai cewa banbanci bai kasance azaba ba bari dai shi yana daga rahama, Allah ya sanya ayoyinsa bayyanannu da wadanda ba bayyane ba domin jarraba mutane har wanda zuciya akwai datti da tsatsa da wanda yake bin shubuha ya bayyana ya fito fili, kamar misalin Kawarijawa da sauran batattun kungiyoyi.

 

Sannan a bayyane yake cewa Allah shine yake da hakkin yin tambaya shi kuma ba a tambayarsa sabida shi mai hikima ne lallai yana ajiye abubuwa a muhallan da suka dace da su, hikimarsa ta hukunta cewa mutum ya kasance cikin jarrabawa a wani lokaci cikin akidunsa wani lokacin cikin ayyukansa kai hatta cikin ibadunsa da dalilansa nassoshinsa na shari’a domin gurbatacce da bayyanu daga mai kyawu gaskiya daga karya, da Allah ya so da ya sanya mutane al’umma gud adaya rak kamar yanda matsarkaki ya fada sai dai cewa hakan yana cin karo falsafa da hikima da ibtila’i (domin ya jarraba ku wanene yafi kyawunta aiki)

Ita duniya makaranta ce cikinta akwai Shugaba da Malamai da Dailbai da darasussuka sannan a karshen shekara akwai jarrabawa domin sanin wanda ya fahimci karatu da kuma wanda ya fadi jarrabawa, ba komai ne yake a bayyane ba dole a samu abinda yake ba a bayyane ba har a gane Dalibi mai kaifin basira da mara kaifin basira,

Alah cikin halittunsa yana da abin ban mamaki daga gareshi muke kuma gareshi zamu koma.

 

Tarihi: [2019/9/17]     Ziyara: [578]

Tura tambaya