mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

TA WACCE HANYA MUTUM ZAI KUBUTA DAGA SHAIDAN DA KAIDODINSA

Salamu Alaikum
Duk yanda na kai da riko da ibada da wani wuridi ko tasbihi da lazimtar karanta ziyarar Ashura da wasunta daga al’amuran ibada sai matsaloli sun dinga faruwa da ni tareda mata ta alal misali sai in dinga afkawa cikin zunubi mai halakarwa ina neman tsarin Allah, babu abinda nake neman daga wannan duniya sai yardar Allah da Annabi da Ahlil-baiti tsarkaka, to ta yaya ne zan samu kubuta daga wannan matsala

 

Salamu Alaikum

Duk yanda na kai da riko da ibada da wani wuridi ko tasbihi da lazimtar karanta ziyarar Ashura da wasunta daga al’amuran ibada sai matsaloli sun dinga faruwa da ni tareda mata ta alal misali sai in dinga afkawa cikin zunubi mai halakarwa ina neman tsarin Allah, babu abinda nake neman daga wannan duniya sai yardar Allah da Annabi da Ahlil-baiti tsarkaka, to ta yaya ne zan samu kubuta daga wannan matsala

 

Babu shakka Shaidan makiyi ga mutum lallai kuma yana madagata yana zuwar ma mutum ta kowanne bangare da geffansa hudu, bai kyale mutum ya kasance bawan Allah bari dai yana son mayar da shi bawansa sai ya dinga jefa masa wasiwasi musammam ma cikin ayyukan kwarai, sai ka ga yana kokarin lalatawa ko dai da riya ko da son daukaka ko shakka da kokwanto ko da aikata zunubi wanda zai goge kyawawan ayyukansa, sai dai cewa tareda haka Allah shi ne mafi jin kan masu jin kai, hakika ya bude kofar tuba da istigfari ga bawansa, lallai kyawawan ayyuka suna tafiya da munana kad aka debe tsammani kada kayi bakin ciki bari dai ka sanya fata da Imani ka dogara da Allah ko da ka gaza cimma nasara to ka kara mikewa ka kirari da yekuwa dan kiran ya Ali lallai shi yana bayyanar da abubuwan ban mamaki da wilayarsa da wilayar ma’abocin zamani dukkanin bakin ciki na gushewa sannan ka yaki zuciyarka da take maka umarni da mummuna lallai makiyarka ce daga cikin gida shi kuma Shaidan la’ananne da sojojinsa daga mutane da aljannu makiyi ne na wajen gida, kada ka sake ka debe tsammani daga rahamar Allah mayalwaciya, ka sanya hasara da kayi ta zama dori ga nasara daga wurin Allah ake samun taufiki dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, matsarkaki ya ce:

 (والذین جاهدوا فینا لنهدینهم سبلنا)

Wadamda suka yi fafutika domin neman yardarmu tabbas zamu shiryar da su hanyoyinmu.

Allah shi ne mai shiryarwa ka nemi taimakonsa ka da ka manta da addu’a Allah madaukakin sarki yana cewa:

 (قل ما يعبؤا بكم ربي لو لا دعاؤكم)

Kace ubangijiku bai damu daku ba don addu’o’inku ba.

Ka roke shi dare da rana domin ya kareka daga sharrukan rai da sharrukan Ashararai da sharrin shaidan daga aljannu da mutane, ka kyautata halayenka tareda iyalansa lallai iyalanka fursunan da ka daure su ne ka tsare.

 

Tarihi: [2019/11/10]     Ziyara: [586]

Tura tambaya