mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Kara kan abin da ka sani a baya cikin ilimin kur’ani mai girma

Hakika ya zo cikin kura’ni mai girma magana kan hasken rana da wata, sai ya bayyana hasken rana ta hanyar Kalmar (ziya’u) ma’ana haske, sannan ya bayyana hasken wata da tanyar amfani da Kalmar (nuru) wacce ita ma’anarta haske, kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:
﴿هُوَ الَّذِي جَعَلَ الشَّمْسَ ضِيَاءً وَالْقَمَرَ نُوراً﴾ .
Shi ne wanda ya sanya rana babban haske da wata mai haskaka

 

Shin akwai banbanci tsakanin Kalmar ziya’u da nuru.

1-ance dukkaninsu kalmomi guda biyu da suke da tarayya cikin ma’ana guda daya, kamar kalmomin mutum da bil adama, ana ambatonsu don nau’antawa.

2-ance suna daga kalmomin da idan suka hadu suke rarraba, idan suka rarrabu suke haduwa, kamar kalmomin fakiri da miskini kamar yadda yake cikin ayar zakka, lallai kalma ta biyu tafi bayyana munanar talaucin matalaucin daga Kalmar farko

3-ance: ziya’u nada ma’anar haske kakkarfa kamar misalign hasken rana da yake haskaka da rana, amma cikin wata haske yana zuwa da ma’anar rarraunan haske da yake haskaka cikin dare.

4-ance: ziya’u yana cikin wanda haskensa ya kasance daga zatinsa kamar misalin rana, sai dai cewa hasken wata bai kasance daga hasken rana sai ya zama daga mai bijiro masa.

5- ance: Kalmar nuru tafi gamewa daga Kalmar ziya’u, sai ya mamaye hasken zati da haske mai bijirowa.

6-ance: hasken rana yana daga mai aiki shi ne ziya’u, hasken wata mai ciraitowa ne kuma yana daga mai karaba shi nuru ne.

7-ance: rana mabubbuga tushen haske ce ma’adanarsa ce, hasken wata yana daga hasken da aka tsiwirta aka nema aka samu daga hasken rana, sai ya zamo daga hasken farko na ziya’u koma bayan na biyu nuru.

Ziya’uya kasantu ga wanda ya zama tushe ga hasken nuru ya kasance daga mai samar da shi da zatinsa kamar yadda yake cikin rana.

bawan Allah Adil-Alawi

 

Tarihi: [2017/12/4]     Ziyara: [738]

Tura tambaya