mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Lallai na kasance mai sabawa iyayena

Salamu Alaikum
Ina ikirari da cewa ni na kasance daga cikin masu sabawa iyayensu ban san yaya ake mu’ama la da mutane ba hatta da mahaifiyata domin lallai ita tana kausasa mu’amala dani bata girmamani a gaban mutane tareda cewa ni ne babban `danta, hakan yayi mini tasiri da canjani ta kai ga bana iyama yi mata biyayya, yanzu ta yay azan iya kasancewa mai mata biyayya tareda cewa ita bata ma yarda ta kyautata mu’amala dani ba?
Allah ya sakawa da su Malam da alherinsa.

Da sunan Allah mai Rahama Mai jin kai

Hakika halin da kake ciki tareda da mahaifiyarka lallai jurewa cutarwar mahaifiya biyayya ce mafi girma, ace ita tana maka mu’amala da kausasawa kai kuma kana kana nuna mata soyayya da girmamata da jin tausayinta da lausasawa da tawali’u, kayi kokarin zama kamar misalin bishiyar Dabino mai kayan marmari zazzaka, duk sanda mahaifiyarka da jefeka da dutsenta da kalmominta masu zafi da kuna da cutarwa kai kuma sai ka dinga bata zazzakan dabiniya, lamarinka ya zama kamar kananan yara da suke jifan Dabino da dutse tareda su samu zazzakan `ya`yan dabino daga bishiyar da suka jefa, lallai kai mutum mafi darajar halittun Allah hakika ya girmamaka kan dukkanin halittu

(لقد كرمنا بني آدم)

Hakika mun girmama Bani Adam.

Kada ka gaza daga gwaggonka bishiyar Dabino cikin kyauta da sadaukarwa da karamci, sannan ka godewa Allah kan misalin wannan Uwa da ya baka da take cutar da kai kai kuma kana hakuri da itam lallai wannan hakuri da kakeyi zai sanya ka cikin Waliyyan Allah daga makusanta zai bude maka duniyar kashafi  da shuhudi ka dinga gani da idanu Barzahu da basira ka dinga ji da kunnen barzahu ya zamana kana ganin abinda sauran mutane basa iya gani kana jin abinda basa iya ji, shaidu da kissoshi nawa na samu daga rayuwar Waliyyan Allah da yanda suka kai ga cimma mukamin fana’i cikin Allah da wanzuwa tareda shi ta wannan hanya ta biyayya ga iyaye da juriya da hakuri tareda su, farin ciki ya tabbata gareka, kayi kokari kaci ganimar wannan lokaci da kwanani tareda mahaifiyarka gabanin ka rasata da yin nadama .

Allah ne mai bada taimako.  

Tarihi: [2021/1/25]     Ziyara: [306]

Tura tambaya