mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin da gaske ne cewa Ayoyi da surorin kur’ani mai girma hadimai, shin su daga Aljannu suke ko daga Mala’iku suke ko kuma dai kawai wannan magana tsuran shaci fadi ce


Salam Alailkum
Shin ya inganta cewa ayoyi da surorin Kur’ani mai girma akwai hadimai shin kuma su daga Aljannu suke ko daga Mala’iku sannan idan wannan magana ta inganta to me ye matsayar shari’a kan neman taimako daga garesu?

 

Salam Alailkum

Shin ya inganta cewa ayoyi da surorin Kur’ani mai girma akwai hadimai shin kuma su daga Aljannu suke ko daga Mala’iku sannan idan wannan magana ta inganta to me ye matsayar shari’a kan neman taimako daga garesu?

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Na’am wannan magana gaskiya ne akwai kebantaccen ilimi da yaa kebantu da su wadanda ake kirga shi daga ilimin Asraru wanda bai saukaka hannun mutane ba, duk wanda ya kasance daga Ahalin wannan ilimi lallai shi ya san hakan ya kuma san yarda zai fito da Mala’iku ko Aljannu daga hanyar Aza’im amma abinda ya fi dacewa gareka ka da ka tsoma kanka cikin wannan ilimi kamata yayi ka yi bincike cikin abinda zai azurtaka cikin rayuwa da yaya rayuwarka za ta kasance rayuwa mai dadi da kyawu domin shi cikin Kur’ani akwai daddadar rayuwa ga wanda yayi imani yayi aiki nagari, aikin nagari nawa ne kake yi a cikin kowacce rana shin kuwa kana sallar dare raka’a goma sha daya cikin lokacin ketowar alfijir shin kana karanta Kur’ani a kowacce rana juzu’i kammalalle da kake hadayar ladna karatun ga Sahibuz zaman amincin Allah ya kara tabbata gareshi har yayi maka addu’a.  

 (اذكروني أذكركم)

Ku tuna dani zan tuna da ku.

Shin kana hidimtawa shari’ar muslunci shin kana yiwa mahaifanka hidima shin kana hidimtawa mutane shin kana hidima ga makusantanka da danginkada makotanka da abokai, lallai mafi alherin mutane shi ne wanda ya amfanar da mutane, ka amsa kira ka roki abinda zai amfaneka duniya da lahira ka da ka tsaya ka dinga bta lokacinka cikin tambayar ayoyi da surori hadimaida cewa shin daga Aljannu suke ko Mala’iku ko mutane, ka taka tsantsan da makiyinka Iblis mai tsananta kiyayya da rundunarsa daga Aljannu da mutane, lallai shi da sunan addini ta iya yiwuwa ya fitar mutum daga addini ya shagaltar da shi da barin mafi muhimmanci bari har mai muhimmancin ya cilla shi kan abinda bai shafe shi ba, me ye ya sanya ka tambaya kan hadiman surori da Ayoyi, mene ne ya hana kai ka kasance cikin hadimai ga surori da Ayoyi, kadai dai ka na wannan tambaya ne kansu saboda kana son amfani da Mala’iku da Aljannu, me ya faru damu muka mantu daga kwanduwa muka jarrabtu da bawon kwai ?

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2018/4/18]     Ziyara: [971]

Tura tambaya