mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Mene ne matsayar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata garesu dangane da Aljanu

Mene ne matsayar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata garesu dangane da Aljanu da wadanda suke da’awar cewa suna da aljanu a jikinsu shin akwai wasu litattafai cikin raddi kan wadannan mutane, da Allah a bamu sunayen litattafan idan zai yiwu

Mene ne matsayar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata garesu dangane da Aljanu da wadanda suke da’awar cewa suna da aljanu a jikinsu shin akwai wasu litattafai cikin raddi kan wadannan mutane, da Allah a bamu sunayen litattafan idan zai yiwu

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Babu abinda ire-iren wadanan mutane suka cudanya da shi da nya wuce wahami, da abinda cikin ilimin mandik ake kiransa da ilimul wahami, lallai yana galaba kan masu raunin zukata a duk sanda inuwa ta surantu gabansu sai su tsammace ta su hiyalinta matsayin Aljani, sannan mu bama inkarin samuwar Aljani hakika Kur’ani ya tabbatar da hakika Aljani da samuwarsa  sai dai kuma Aljani bashi da wani iko da karfi kan mutum (ban halicci Aljani da mutum face don bauta mini), (yaku taron mutum da Aljan idan kuna da dama….) (kace an mini wahayi cewa wasu jama’a daga Aljanu).

Sannan ka duba littafin 1- Maratibul Wa Aja’ibul Jinni kama yusawwiruhu Kur’an was sunna, wallafar Wajadud dini Shibili daya daga malaman karni na takwas, 2 Lu’u’lu wal Murjan fi Ahkamil Jani: Jallaluddini Suyudi,3 Aljinni baina Haka’ik wal Asadir; Aliyu Jundi, 4 Alamul Jinni wal Mala’ika: Abdur-Razak  Naufali, 5 Alamul Jinni Wal Shayadin; Umar Ash’har 6 Risalatu fi Tarjamanil Jinni: Yusuf Kunsari.

Tarihi: [2021/3/27]     Ziyara: [311]

Tura tambaya