mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

ME AKE NUFI DA (YA ALLAH INA ROKONKA DA SUNAYENKA DA MAFI GIRMANSU DA DUKKANIN SUNAYENKA MASU GIRMA

Salamu Alaikum wa Rahmatullahi wa barakatuhu Allah ya datar da ku zuwa ga abinda yake so yake yarda da shi.
Akwai wani layi da ya zo cikin Du’a’ul Baha’i

(اللهم اني اسالك من اسمائك باكبرها وكل اسمائك كبيرة اللهم اني اسالك باسمائك كلها)
Ya Allah ian rokonka daga sunayenka masu girma da mafi girmamarsu da dukkkanin sunayenka masu girma ya Allah hakika ina rokonka da dukkanin sunayenka.

Daga fuskanin Imam amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yana cewa akwai wasu sunaye mafi girmama daga cikin sunaye wannan ishara ce zuwa cewa akwai Ismul A’azam da dukkanin sunaye suke shigewa karkashinsa, ta wata fuskar kuma Imam (a.s) yana cewa: dukkanin sunayen Allah suna da girma a wannan fage akwai wani hadisi na Annabi (s.a.w) da yake bayanin cewa babu wani suna wai shi Ismul A’azam kadai abin bukata shine ka karkade duk wani abu da ba Allah daga cikin zuciyarka ka roke shi da dukkanin sunan da kake so wannan shine Ismul A’azam, karkashin wadannan abubuwa guda biyu mene ne hakikar lamari tabbatacce?a aya ta takwas daga Suratul Muzammil:

 (واذكر اسم ربك وتبتل اليه تبتيلا)

Ka ambaci sunan ubangijinka ka yanke zuwa gareshi yankewa.

Daya daga cikin ma’anonin tabattul shine yankewa zuwa ga Allah ta’ala hadisin Annabi (s.a.w) yana bayani da cewa ka karkade zuciyarka daga duk wani abu da yake koma bayan Allah ka roke shi da dukkanin sunan da kake so, shin wannan aya mai daraja tana dacewa da ma’anar wannan hadisi mai daraja, lokacin da na tsaya na zurfafa tunani cikin wannan aya sai wadanna tambayoyi suka fado cikin tunani na, lallai muna cikin tsananin kishirwa neman amsa da samun ilimi da ma’arifa ku taimaka ku fa’idance mu Allah ya dawwamar da albarkarku don darajar Muhammad da iyalansa tsarkaka (a.s)

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Hakika na rubuta sharhi kan Du’a’ul Sahar haka zalika ina da laccoci kai da tashar tauraron dan Adam mai suna Alma’arif ta yada shirin tsahon shekaru biyu a watannin Ramadan mai Albarka. Ka na iya koma ka duba idan kana bukatar bayani filla-filla.

Bugu da kari na ambaci Ismul A’azam da sauran sunayen Allah

Tarihi: [2019/11/6]     Ziyara: [535]

Tura tambaya