b DA WACCE KA’IDA ZAMU IYA SANIN INGANCIN WURAREN ZIYARA YA ZUWA MA’ABOTANSU
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

DA WACCE KA’IDA ZAMU IYA SANIN INGANCIN WURAREN ZIYARA YA ZUWA MA’ABOTANSU


Salamu Alaikum wa Rahmatullahi wa barakatuhu
1-Da wadannne ka’idoji ne zamu iya sanin ingancin wuraren ziyara ya zuwa wadanda aka danganta su zuwa garesu? Shin shuhura hujja ce a wannan mukami?
2-shin kuna yankewa kan ingancin danganta Kabarin Hamzatul Garbi wanda yake kudancin garin Hilla da yake Iraki ya zuwa ga marawaici Sika

 

Salamu Alaikum wa Rahmatullahi wa barakatuhu

1-Da wadannne ka’idoji ne zamu iya sanin ingancin wuraren ziyara ya zuwa wadanda aka danganta su zuwa garesu? Shin shuhura hujja ce a wannan mukami?

2-shin kuna yankewa kan ingancin danganta Kabarin Hamzatul Garbi  wanda yake kudancin garin Hilla da yake Iraki ya zuwa ga marawaici Sika –ta yanda Najjashi ya yi bayaninsa ya kuma wassaka shi da cewa shine Hamzatu ibn Kasim ibn Alhassan ibn Ubaidullahi ibn Abu Fadalul Abbas Amincin Alllah ya kara tabbata a gareshi , dole ne ayi ishara zuwa ga abubuwa biyu danganta wannan wurin ziyara da kabarin Hamzatul Garbi kissa mai tsayi ta zo kansa Mirza Nuri ya kawo ta cikin littafinsa mai suna Jannatul Ma’awa sh 119, hakama cikin littafin Biharul-Anwar J 53 sh 286 da Assayidul Shirazi cikin littafin Min Karamatul Auliya, da yawan malamai sun danganta wannan wurin ziyara zuwa ga Hamzatul Garbi, kamar misalin Assayidul Kuyi cikin littafin Mu’ujamul Rijal, Almuhaddisul Qummi cikin Alkuna wal Alkam da Aga Buzurgi Teherani cikin ba’arin litattafansa kamar misalin Azzari’atu da Musaffa da Makalu, da Allama Mamakani cikin Attankihul Makal da Mir’atul  Kamal da Assayidul Hassan Sadru cikin Ta’asisul Shi’a, da Shaik Hirzuddini cikin Marakidul Ma’arif da sauransu.

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Dangane da Shariftaka cikin daidaiku kadai dai an tafi kan hakan cikin tabbatar da ita ta hanyar shuhura  takardar da nasaba ma na karfafata daga fuskanin kwararrun masana, amma wuraren ziyara dangane da su ana komawa ne wurin gogaggun masana da dandake batun da masana wannan fanni sai dai cewa ni bana daga cikinsu amma fa ina ziyartar wuraren ziyara ko da kuwa isnadinsu raunana ne da cikin tarihi lallai ni ina wadatuwa da danganta kabarin zuwa ga Ahil-baiti Amincin Allah ya tabbata a gare su, kamar dai tutar da ake daga ta sama dauke da sunansu duk da cewa daga kyallen yadi take sai dai cewa yayinda aka danganta ta ga Abul Fadlul Abbas raina fansarsa amincin Allah ya tabbata a gare shi to zan girmamata kuma zan nemi tabarruki da ita.

Wurin Allah muke neman taimako
Tarihi: [2019/10/19]     Ziyara: [529]

Tura tambaya