mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wane ne Abu Hamza Assumali

Menene ainahin sunan Abu Hamza Assumali?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya zo cikin littafin Mu’ujamu Rijalu Hadis na Sayyid Ku’I (Ks) juz 3 sh 385: shine Sabitu Ibn Dinar wanda ake wa Alkunya da Abu Safiyya  shi sika ne yana kuma da littafi, Najjashi yace: Sabit Ibn Abu Safiyya Abu Hamza sunansa Abu Safiyya Dinar, ma’abocin wilayar Ahlil baiti kuma bakufe, sika, `ya`yansa sune Nuhu da Mansur wadanda aka kasha su tareda Zaidu, ya hadu da Aliyu bn Husaini  da Abu Jafar Imam Bakir da Abu Abdullah Imam Sadik da Abu Hassan Imam Kazim (as) ya rawaici Hadisi daga garesu ya kasance daga mafi alherin sahababban su da sikarsu ababen dogaro cikin riwaya da nakalto hadisi, an arawaito daga Abu Abdullah (as) fadinsa: Abu Hamza cikin zamaninsa misalin Salmanu ne cikin a zamaninsa, wasu daga Ahlus-sunna sun rawaito daga gareshi, ya mutu a shekara ta 150 bayan hijir, ina ma mu kasance Salmanu zamaninmu cikin zamaninsa wurin maulanmu Sahibul Amri (as)

Idan kana bukatar Karin bayani kana iya komawa ga littafin A’ayanul shi’a wallafar Sayyid Amir (Ks). 

Tarihi: [2019/4/16]     Ziyara: [511]

Tura tambaya