mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

RIWAYA DA ISNADINTA ZUWA GA MANZON ALLAH (S.A.W)

Salamu Alaikum akwai wata riwaya da ake ambata ake dangane isndinta ga Manzon Allah (s.a.w) yace: mumini yanada labule dai`dai` har guda 70 idan ya aikata zunubi sai labule gud aya kece daga gareshi, amma idan ya tuba sai Allah ya dawo masa da shi tareda guda bakwai, idna kuma yaki tuba ya kafe kan aikata zunubi da sabo sai baki dayan labulayen su kekkece ya wayi gari babu lullubi da labule gareshi, Allah yayi wahayi ga Mala’ikunsa ku suturce bawana da fukafukanku, lallai shi `dan Adam basa canjawa sai dai su tozarta, ni kuma ina canjawa bana tozartarwa, idan yaki ya kafe sai cigaba da aikata sabo sai Mala’iku su kai kara wajen uabngijin su janye fukafukansu su ce: ya ubangiji lallai wannan bawan naka hakika mun gabata daga abinda yake aikatawa daga alfasha daga abinda ya bayyana daga gareta da wanda ya buya, yace: sai Allah ta’ala yace: ku dauke fukafukanku, da zai aikata kuskure cikin duhun dare ko hasken rana ko cikin daji ko cikin kasan ruwa da Allah ya zartar da shi kan harsunan mutane, ko roki Allah ta’ala da kada ya keta labulanku ya tona muku asiri.
Shin wannan riwaya tana nuni da cewa Kenan Allah ya na tona asirin mumini mai yawan aikata sabo Ashe Allah bashi ne mai yawan suturce aibobi ba.

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Na’am shine mai suturce aibobi sai dai cewa da sharadi da sharuddanta daga cikin sharadin shine bawan ya zama ya ji kunyar ubangiji ya kauracewa cigaba da aikata sabo ta yanda ba zai jawo masa kekkecewar suturarsa da labulayensa ba, a hakika Allah bai tona masa asiri ba shine ya taonawa kansa asiri(abinda ya sameku daga musiba ya kasance daga kawukanku kuma Allah yana afuwa daga abubuwa masu yawa)

Tarihi: [2019/12/14]     Ziyara: [573]

Tura tambaya