mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Gwajajjiyar addu’a da aka gwada domin samun daukar ciki da samun zuriya.

Salamu Alaikum ni sharifiya ce nai aure sannan ina da diya da shekarunta ya kai takwas da haihuwa tun bayan haihuwarta Allah bai kara kaddara mini samun haihuwa ba saboda matsalar da mijina yake tattare da ita da nesantarsa daga ubangiji ina rokon addu’a daga gareku da zata shiryar da mijina daga nesantar miyagun abokai da kuma addu’ar samun azurtuwa da zuriya.
Allah ya saka muku da alheri ina sauraron amsarku.

da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ina rokon  Allah subhanahu wata’ala da ya azurtaki da zuriya saliha ya kuma shiryar da mijinki zuwa ga imani kammalalle da aiki nagari,

Mutane baki dayansu suna cikin hasara face wadanda sukai imani sukai aiki nagari.

 (والعصر إن الإنسان لفي خسر إلّا الذين آمنوا وعملوا الصالحات وتواصوا بالحق وتواصوا بالصبر)

Ina rantsuwa da zamani lallai mutum yana cikin hasara face wadanda sukai imani sukai aiki nagari sukai wasicci da gaskiya sukai wasicci da hakuri.

Ita hasara shine uwar kudi jari ta tafi da kuma ribarsa.

 Allah ya bamu jari mai girma shine rayuwa da lokacinmu idan ya zamanto bamu amfana daga rayuwarmu ba cikin biyayyar Allah mun rabauta mun samu tsira ba cikin duniya da lahira mun shiga aljanna da koramu ma’ana mun kasance daga masu tsoran Allah cikin aljannoni da koramu wurin sarki mai ikon yi a matsugunin gaskiya ba to da mun tafka hasara  ga rayuwarmu ranar kiyama lokacin da za mu ga wutar jahannama kamar yadda ya zo cikin suratu fajar da mun ce:

 (ياليتني قدّمت لحياتي)

Ina ma na gabatar ga rayuwata.

Rayuwar hakika ita ce rayuwar lahira ta har abada wacce babu mutuwa cikinta, ya zama wajibi muyi tanadin guzuri da abin hawa zuwa ranar kiyama wand ashine imani cikakke da tauhidi da annabta da imamanci da aiki nagari

 (إليه يصعد الكلم الطيب والعمل الصالح يرفعه)

Zuwa gareshi daddadan zance ke daukaka kuma aiki nagari yake daukaka shi.

Ki karanra wasikata wannan yar kaskantatta kan mijinki mai girma tsammani kalma ta shiga zuciyarsa ta canja rayuwarsa daga mummuna zuwa kyawu daga kyawu zuwa mafi kyawu hakai dai har ya kai ga zuwa ga Allah lallai shi mai haduw ada shine

 (يا أيها الإنسان إنّك كادح إلى ربك كدحاً فملاقيه)

Ya kai mutum lallai kai mai dawainiya ne zuwa ga ubangijinka dawainiya tabbas zaka hadu da shi.

 و(إلى ربّك المنتهى)

Kuma zuwa ga ubangijinka magaryar tukewa take.

 و(إنا لله وإنّا إليه راجعون)

Daga Allah muke kuma gareshi zamu koma.

Dukkaninmu zamu koma zuwa ga Allah da haduwa da shi sai dai cewa daga cikinmu akwai wanda zai hadu da Allah da mafi rahamar masu rahama idan ya kasance daga muminai daga cikinsu kuma akwai wanda zai hadu da shi da mafi tsananin masu ukuba cikin wurin azaba da fansa idan ya kasance daga masu sabo da fasikai da dawagitai azzalumai, babu tsimi babu dabara face ga Allah madaukaki mai girma

Tarihi: [2018/3/18]     Ziyara: [3248]

Tura tambaya