mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

INA SON MALAM YAYI MINI BAYANI WANNAN RIWAYA DA ZATA ZO A KASA


Salamu Alaikum
Ina fatan Akaramakallahu zai mini bayani a sharhin kan wannan riwaya shin akwai wata duniya da waninmu ya sameta
Shaik Saduk cikin littafinsa (Attauhid sh 277)

 

Salamu Alaikum

Ina fatan Akaramakallahu zai mini bayani a sharhin kan wannan riwaya shin akwai wata duniya da waninmu ya sameta

Shaik Saduk cikin littafinsa (Attauhid sh 277)

((أبي رحمه الله قال: حدثنا سعد بن عبد الله قال حدثنا محمد بن عيسى عن الحسن بن محبوب عن عمرو بن شمر عن جابر بن يزيد قال: سألت أبا جعفر (عليه السلام) عن قوله عز وجل: (( أَفعَيينَا بالخَلق الأَوَّل بَل هم في لَبس من خَلق جَديد )) (قّ:15), قال: يا جابر تأويل ذلك أن الله عز وجل إذا أفنى هذا الخلق وهذا العالم وسكن أهل الجنة الجنة وأهل النار النار جدد الله عالما غير هذا العالم وجدد خلق من غير فحولة ولا إناث يعبدونه ويوحدونه وخلق لهم أرضا غير هذه الأرض تحملهم وسماء غير هذه السماء تظلهم لعلك ترى ان الله إنما خلق هذا العالم الواحد وترى إن الله لم يخلق بشراً غيركم بل والله لقد خلق الله ألف ألف عالم وألف ألف آدم أنت في آخر تلك العوالم)).

Ubayyu Allah ya yi masa rahama yace: Sa’ad Ibn Abdullahi ya zantar damu ya ce Muhammad Ibn Isa daga Hassan Ibn Mahbubu daga Amru Ibn Shimru daga Jabir Ibn Yazid yace na tambayi Abu Jafar (a.s) dangane da fadinsa Azza wa Jalla: (yanzu mun gaza ne da halittar farko bari dai su suna cikin rudu daga sabuwar halitta) suratu Kafu:15, ya ce: hakan ya kasance idan Allah ya karar da wannan halitta da wannan duniya ya sauke yan aljanna cikin aljanna ya zuba yan wuta a wuta Allah sai ya sabunta wata duniya koma bayan wannan duniyar ya sabunta halittu ba tareda namiji da mace ba zasu dinga bautawa masa suna dayanta shi sannan ya shimfida musu wata kasa koma bayan wannan kasar da zata dauke su ya kuma kagar musu sama koma bayan wannan da zata lullufe su ta yiwu kayi tsammani cewa kadai dai Allah iya wannan duiyar ya halitta guda daya, kuma ta iya yiwuwa kayi tsammanin Allah bai halicci wasu mutane ba koma bayanku, bari dai abin ba haka yake ba hakika Allah ya halicci dubun dubatar duniyoyi da dubunnan Adamu kai kana cikin na karshen wadannan duniyoyi.

 

Ina fatan Akaramakallahu zai yi mini sharhin wannan hadisi shin wasunmu sun samu wata duniya koma bayan wannan duniyar da muke ciki.

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Zahirin abinda hadisin yake nuni gareshi bayan tabbatuwar ingantarsa shine cewa akwai wasu duniyoyi gabaninmu da bayanmu,

Allah ne masani.  

Tarihi: [2019/12/4]     Ziyara: [576]

Tura tambaya