mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Matsayin mace a Al’uma

Assalamu alaikum
Akwai wani abun da ke damuna sosai ina neman cikakken bayani akan sa domin mu daliban ilimi ne, zamu ga mace a cikin al’uma tazamo wata wato zakaran gwajin dafi cikin hukumar kasa har takan sha gaban namiji, sannan mun san cewa wani ayyukan dole ne su matan ne kawai zasu iya, hakan ya sanya cakuduwan mata da maza cikin daula, wannan wani abun tsoro ne, ina neman Karin bayani akan hakan, sannan ina neman nasihar ku kan auran matar da take aiki a hukuma.

Da sunan Allah me rahama me jin kai

Abin cewa anan shine in dai ba wani abun da zai janyo fasadi ko zargi da tuhuma ba to ba wani matsala

Sanann bisa maganar zabar mace ya kamata ka zabi matar da take daidai kai ne domin shi aure kamar kara karfin tantame igiya biyu ne, don haka duk wanda suka kasance suna da kusanci da juna tantamewar su zai fi karfi, amma idan har ya kasance daya daga cikin su igiya ne dayan kuma kamar zare ne toh lallai wannan dauri bazai tantamu ba ko ba zaiyi karfi da kwari ba kuma cikin kankanin lokaci zai yanke.

Tarihi: [2016/11/20]     Ziyara: [962]

Tura tambaya