mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin akwai wani dalili yankakke da ke tabbatar da haramcin wa`ke

Shin da gaske ne babu wani dalili kan haramcin wa`ke saboda ba a ambaci wa`ke ba cikin kur’ani

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Hakika an ambaci wa`ke cikin kur’ani cikin fadinsa madaukaki:

 (واجتنبوا قول الزور(

Ku kauracewa zancen kage.

Lallai yadda al’amrin yake shi ne ya zo cikin tafsirin wannan aya wajen jamhur din malaman shi’a da sunna cewa daga zancen kage shi ne akwai wa`ke-wa`ke, kammar yadda ya zo cikin fadin Allah cikin kur’ni mai girma:

(ما أتاكم الرسول فخذوه وما نهاكم عنه فانتهوا)

Duk abin da abin da annabi ya zo muku da shi kuyi riko da shi duk abin da ya haneku ku hanu.

Hakika gomomin riwayoyi sun zo daga annabi (s.a.w) cewa haramcin wa`ke-wa`ke kuna iya komawa littfai da sukai bayani kan hakan filla-filla cikin wannan babi.

Dukkanin abin da manzon Allah (s.a.w) ya fada to Allah ya fade shi duk wanda ya yiwa manzon Allah (s.a.w) biyayya Allah ya yiwa biyayya. Babu shakka kan haramcin wa`ke Allah abin neman taimako
Tarihi: [2017/7/22]     Ziyara: [860]

Tura tambaya