mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Balagar yara

Salamu Alaikum
Ni matashi ne da nake da shekara goma sha uku sannan gashi ya tsiro a marata kuma na fitar da maniyyi ta hanyar wasa da ala’aura sai dai cewa tareda wadannan abubuwa guda biyu har zuwa yanzu gashin hammata bai tsiro mini ba kuma banyi mafarki da mace shin na balaga Kenan ko ban balaga ba?

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Ana gane balaga da daya da abubuwa guda uku:

1-cika shekaru goma sha biyar

2- tsirowar gashin mara mai kaushi

3-mafarki da mace ko kuma fitar maniyyi, saboda haka kai ka balaga da alama da uku , sannan ka dena wasa da al’aurarka lallai yin hakan haramun ne kuma zai kaika ga shiga wuta da fushin Allah, kada ka fusata ubangijinka wanda ya baka dukkanin ni’ima , ka gode masa ta hanyar barin aikata waccen mummunar al’ada da dukkanin ayyukan haramun, sannan wajibi ne a kanka ka sauke ayyukan wajibi ka roki ubangiji ya datar da kai da rayuwa mai tsafta tsarkakka da take cike da farin ciki ka kuma kasance daga wadanda suke hidimatawa addini da mazhaba da mutane da kasarka, ka da ka bata samartakarka ka karar da ita cikin ayyukan sabo lallai zunubi yana jawo wa mutum tsiyata a duniya da lahira.

Wurin ubangiji muke neman taimako.

Tarihi: [2020/9/8]     Ziyara: [535]

Tura tambaya