mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

mecece falsafar samuwar imam?


1-me yasa Allah mai girma da daukaka ya halicci mutum?
2-bukatarmu zuwa ga jagorori na Allah?
3- mecece falsafar samuwar imam?
4- mecece falsafar samuwar mai kawo gyara mai girma ga duniya da kuma fakuwarsa?

 

mecece falsafar samuwar imam?


1-me yasa Allah mai girma da daukaka ya halicci mutum?

2-bukatarmu  zuwa ga jagorori na Allah?

3- mecece falsafar samuwar imam?

4- mecece falsafar samuwar mai kawo gyara mai girma ga duniya da kuma fakuwarsa?

 

Da sunansa mai rahama mai jin kai

 

Tabbas Allah shi ne kamala tsantsa daga kamalar kamala tsantsa kamalarsa ta kwarara, kamar yadda daga kamalar rana tarsashin haskenta ya kwarara ya samu, sai Allah ya halicci halittu daga kamalar kamala, kamar yadda ya zo cikin hadisil kudsi daga Allah matsarkaki

>كنت كنزاً مخفياً فأحببت أن اُعرف فخلقت الخلق لكي أعرف.

Na kasance boyayyiyar taska sai na so a sanni sai na halicci halittu don a sanni.

Sanin kamala da larura yana hukunta abin da yake nuni zuwa ga kamala, halittar ayoyin sasanni da numfasoshi sun nuni kan samuwar kamala tsantsa masanin komai mai iko kan komai rayayye tsayayye daya makadaici wanda babu wani abu kwatankwacinsa, sannan su halittu sun banbanta  bisa la’akari da illoli da ma’alulai sakamakon ka’idar mafi daraja hakika mafi daraja mai daraja da makusanci na fitowa daga cikinsa wannan na lazimta saukar silsila cikin bakan nuzuli har sai ya sauka kan mafi Kankan da koma bayansa, mafi darajar halittar Allah shine Muhammad da iyalan gidansa wanda ake kiransa a wajen arifai da sunan hakika muhammadiya, lallai shi ne mai gangarowa na farko daga Allah matsarkaki

 (أول ما خلق الله نوري)

Farkon abin da na halitta shi ne haskena.

Shi ne hankali na farko sannan kuma daga baya sauran hankula suka sauka da martabobin samuwa daga mafi daukaka zuwa madaukaki ya zuwa na makaskanci wanda tamatansa shi ne duniya mafi kasa-kasa wacce muke rayuwa cikinta, sai Allah ya halicci mutum domin ya zamanto halifan Allah cikin halittarsa ya kasance mazhari mabayyana ga sunansa mafi girma ga sunayensa mafi kyawu da siffarsa madaukakiya, mutum shine mafi daraja da daukakar Allah ya bijirar da amana ga halittunsa sune taklifin shari’a sai sammai da kasa suka ki daukar amanar sai mutum ya dauk, sai ya kasance mahallin wazifofin addini da taklifin Allah da wannan ne mutum ya daukaka kan ragowar halittun Allah saboda shi yana dauke da hankali wanda yake ga mala’iku da nafsu wadda dabbobi ma suna da ita, idan hankalinsa yayi galaba sai ya kasance mafi falala da daraja daga mala’iku bari mala’iku ne zasu dinga yi masa hidima, idan sha’awarsa a nafsu mai yawan umarni da mummuna tayi galaba sai ya kasance kamar dabbobi bari dai mafi batan hanya daga dabbobi.  

 Allah ya shiryar da mutum ko dai ya kasance mai godiya ko kuma mai kafircewa sai ya saukar da litattafai ya aiko da manzanni domin shiryar da mutane da farin ciikinsa domin ya isa ga kololuwar kamalarsa  shi ne mukamin fana’I  cikin Allah da wanzuwa tare da shi, wajibi kanka ya kai mutum ka kai ga wannan mukami da matsayi shin ka taba tunanin haka ko kuma har yanzu baka gushe ba kana tunani me yasa Allah ya halicci mutum?

2- daga cikin amsa ta farko aka san jawabi ta biyu a jumlace lallai mutum ya harhadu daga hankali da sha’awa ne da nafsu mai yawan umarni da munana wacce take fisgarsa zuwa ga ayyukan sabo da sha’awe-sha’awe na haramun da zunubai da karkata da bata da tsiyata Allah mai tausayi mai shiryarwa mai nusantarwa yana son bayinsa  yana nfin alheri garesu da farin ciki sai ya aiko musu jagorori na Allah domin shiryarsu domin sanar da su alheri daga sharri da gaskiya daga bata da wahayi zai taimakwa hankalisa don rayuwa mai kyau don farin ciki duniya da lahira, kamar yadda Allah ya turo manzanni da annabawa da jagorori na Allah domin hujja cika hujja kan mutane domin kada mutane bayan haka kada su samu damar fadin da dai Allah ya aiko mana da manzanni domin mu shiriya, masu bushara da gargadi domin mutane su tsayu da adalci.

3- amsa: tabbas ya tabbatu a muhallinsa ba da ban hujja ba da kasa ta nutse da wanda ke kanta, wanzuwar tsarin halitta da na shari’a kadai dai da samuwar hujjar Allah kan halttun Allah cikin kowanne zamani sai dai cewa hujjar Allah wani lokaci mabayyaniya wani lokaci fakakkiya kamar fakuwar rana bayan girgije, lallai arana tanada tasirinta hatta lokacin fakuwarta  ya zuwa haskakarta da hudarta a lokacin girgije zai kwansare haka lamarin yake dangane da mai kawo gyara a duniya baki dayanta  hujjar Allah kan halittunsa, lallai yana da tasirin hujjntaka ko da kuwa yana halin fakuwa, lallai mu muna jira da tsimayin hudowar ranarsa domin ya cika kasa da adalci da daidaito kamar yadda ta cika zalunci da danniya.  

Allah ya sanya mu tare da dukkanin muminai daga cikin masu saurare da tsimayi na hakika daga mafi alherin shi’arsa da masu shahada gabansa

 

Tarihi: [2017/8/29]     Ziyara: [788]

Tura tambaya