mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wani ne yake cewa wai shi yana haduwa da Imam Mahadi A.F

Salamu Alaikum
Akwai wani mutum mai suna Ali Haidar Ali yana da tasha a dandalin sadarwa na Telegram yana watsa shirye shirye da labaran duniya da muzaharori da suke kifar da hukumomi da Dauloli, yana bada labari ta hanyar ilimin (parapsychology) yana nakaltowa ta hannun wani da ake kira Aub Turba wand ayake da’awar ganawa da Imam Mahadi Allah ya gaggauta bayyanarsa, mene ne ra’ayinku dangane da wannan mutumi.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Aimin uzuri ina neman afuwa lallai ni bansan wannan mutumi da kake Magana kansa ba, sannan mu muna tareda dalili ne duk inda ya karkata can zamu karkata, bama karbar duk wata da’awa daga kowanne mutum sai bayan mun samu kwararan dalilai daga littafin Allah da sunnar Annabinsa da minhajin Ahlinsa tsarkaka da sirar Malamanmu manyan masana.

Allah ne mai taimako.

Tarihi: [2021/4/27]     Ziyara: [454]

Tura tambaya