b ME YASA IMAM ALI BA TASHI YA DAUKI FANSAR ZALUNCIN DA AKAIWA FATIMA A.S BA
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

ME YASA IMAM ALI BA TASHI YA DAUKI FANSAR ZALUNCIN DA AKAIWA FATIMA A.S BA

Salamu Alaikum
Me ya sa Imam Ali (a.s) bai tashi ya dauki fansar zaluncin da aka yi kan shugabarmu Mazluma (a.s) da karfi ba, me yasa bai dawo da gonar Fadak ba da karfi ba kamar yanda aka kwaceta da karfi? Ina Sahabbai masu daraja da musulmi suka kwana daga baiwa shugabar matayen duk duniya kariya, Ina Abu Zar? Ina Salmanul muhammadi? Ina sauran masu daraja?

 

Salamu Alaikum

Me ya sa Imam Ali (a.s) bai tashi ya dauki fansar zaluncin da aka yi kan shugabarmu Mazluma (a.s) da karfi ba, me yasa bai dawo da gonar Fadak ba da karfi ba kamar yanda aka kwaceta da karfi? Ina Sahabbai masu daraja da musulmi suka kwana daga baiwa shugabar matayen duk duniya kariya, Ina Abu Zar? Ina Salmanul muhammadi? Ina sauran masu daraja?

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Juyi da saura suna tabbatuwa ne lokacin da mazaje kwami da tarin mutanenta masu iklasi da sadaukarwa suka samu, abinda ya zama wajibi shine abubuwa su tabbatuwa da yanayinsu na dabi’a, juyi kan Azzaluman mahukunta da wadanda suke rike da madafan iko da dukkanin mabiya jahilai ya zama wajibi ta kasance cikin karatun nutsuwa a tsanake a tsare da kyawuntar yanayi, misalin hakan bai samu tabbatuwa bayan taron Sakifa.

Sarkin muminai (a.s) ya wanzu shi kadai abin zalunta yana kewaye da mataimaka da basu wuce yatsun tafin hannu ba, kai hatta Sayyada Fatima (a.s) tareda `ya`yanta ta kasance cikin dare tana yawo lungu lungu don neman mataimaka sai suyi mata alkawarin zasu zo su taimaka sai dia cewa abin ban takaicin basu cika alkawari babu wanda ya fito da askakken kai don cika alkawari in banda Salmanu da Abu Zar, (`yan kadan daga bayina masu godiya) mafi yawan su batattu ne da wanda Allah yayi fushi kansu, ta kaka zai yunkura ya tashi don kwatar hakki, sannan ba za a kiyasta shi da yunkuri da Imam Husaini (a.s) yayi ba, domin kowanne mutum da irin yanayin da yake samun kansa,nataijar yunkurinsa ya samar da  shahadar Imam Husaini da nasarar da jini yayi kan takobin Umayyawa, misalin wannan lamari bai samu ba cikin yunkurin Alawiyya fatimiyya,

Amma batun Fadak labarin na da mai bakanta zuciya kuna iya duba littafin Shahid Sadar (ks) da littafin Asraru Fatima da `danmu Ruhani Shaik Fadil Mas’udi (d.z)



Tarihi: [2019/11/3]     Ziyara: [536]

Tura tambaya