mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

DANGANE DA INGANCIN ISNADIN HUDUBA TA 55 CIKIN NAHJUL BALAGA

Salamu Alaikum
Hakika na shiga cikin matukar damuwa yayin da na kasa bada amsa ga daya daga cikin abokaina yayin da ya tambayeni gameda ingancin isnadin hudubar Imam Ali (a.s) cikin Nahjul Balaga lamba 55 inda Imam (a.s) yake cewa:
{ ولقد كنا مع رسول الله-ص-نقتل أبناءنا وآباءنا..الخ }
Hakika mun kasance tare da Manzon Allah (s.a.w) muna yakar `ya`yanmu da iyayenmu …….
Akaramakallahu ku tallafa mana da bayani Allah ya kara muku kariyarsa,

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Yana Magana ne da yawun wasu ya kasance a yakokin da suka gabata tsakanin musulmi da mushrikai kamar misalin cikin yakin Badar zaka samu musulmi yana yakar dansa kafiri haka `da musulmi yana yakar babansa kafiri, wannan Magana ishara ce ga hali na karfi da dakiya cikin Imani, zaka iya komawa ga sharhohin da aka rubuta kan Nahjul Balaga kamar misalin Sharhu Ibn Abil Hadidi da na Assayid Ku’i da wasunsu daga Sharhohin da malaman sunna da shi’a suka yi akai.

Tarihi: [2019/11/27]     Ziyara: [460]

Tura tambaya