mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

hukuncin hankali na aiki

Akwai wani hukunci wanda yake karkashin hukuncin hankali na aiki wanda ake iya sabani a kansa, misali a babin fadadawa za mu ga hukuncin siyasa shi ma hukunci ne na hankali na aiki, da lamarin da ya shafi dokoki na


Akwai wani hukunci wanda yake karkashin hukuncin hankali na aiki wanda ake iya sabani a kansa, misali a babin fadadawa za mu ga hukuncin siyasa shi ma hukunci ne na hankali na aiki, da lamarin da ya shafi dokoki na hakkokin al’umma Kotu dukkaninsu suna karkashin hukuncin hankali na aiki, haka ma abin da ya shafi tattalin arziki shima dokokin hankalin aiki suna shiga cikinsa domin bayani mai kyau da mara kyau, haka ma abin da ya shafi zamantakewar al’umma hankalin aiki nan ma na shiga ciki, dokokin sa suke karkashin Doka hatta da Kotu da Kurkuku da sauransu duk suna shiga karkashin hukuncin hankali.

Akwai hukunci na shari’a kuma, hukuncin shari’a a nan mun takaita da wanda addini yayi nuni da shi kai tsaye ba tareda nuni da dokokin kasa da kasa na duniya da ake amfani da shi yana iya zama hukunci amma ba a kiransa da hukuncin shari’a sai dai hukuncin dokokin kasa da kasa kuma hankula ke amfani da shi karkashin hukuncin hankali na aiki, anan zamu fahimci hukuncin doka tsakanin kasa da kasa na shiga siyasa Kotu fursun da sauransu.

Abinda ake nufi da hankalin aiki shine hankalin da yake siffanta aiki  mai kyau ne ko mara kyau, shi ya sanya zamu ga hankalin aiki na shafar komai da komai baki dayan rayuwar mutum.

Hukuncin shari’a d amujka ce muna nufin addini da ma’anarsa takaitacciya mara fadi shine wannan hukunce-hukunce da suka shafi dukkanin fagagen da hankalin aiki ke shiga ciki.

Duk inda hankalin aiki ke shiga shima hukuncin shari’a ma yana shiga.

An kasa hukuncin shari’a zuwa ga hukunci wada’i da taklifi,

Wada’I na nufin hukuncin da ake sanyawa, misali kan hukunci Wada’i, shine kamar mika kaya da ciniki dole kafin ya tabbatu a mika kaya sannan a karbi kudi wannan ko da babu shari’a haka masu hankali suke tafiya kai.

Amma Hukunci Taklifi shine hukunci da yake ta’allaka da aikin mutum kai tsaye ba tareda wasida ba, sabanin Wada’i da yake kallon yanayi sabubba sharudda  da sauransu, sai a kira shi da hukunci Wada’I wanda kafin shari’a dama can haka rayuwar mutane take sai shari’a ta zo ta karfafe shi ta bashi wani hukunci.

Tarihi: [2018/4/8]     Ziyara: [758]

Tura tambaya