mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Riwayar da aka nakalto daga Rida (as): duk wanda ya tsarkake kansa daga waka lallai…

Salam Alaikum
Akwai daga Imam Rida (as) da take cewa: duk wanda ya tsarkake kansa daga waka lallai cikin aljanna akwai wata bishiya da take motsa sautinta da bata taba jin irinsa…. Har zuwa karshen riwayar, riwaya ta biyu itace:

ورواية قال الاعرابي يا رسول الله هل يوجد في الجنة غناء قال رسول نعم يااعرابي ان على طرفي نهر الجنة ابكار بيضوات يتغتين با اصوات لم يسمع الخلائق مثله قط قال بتسبيح.
Wani balaraben kauye yace ya manzon Allah shin a aljanna akwai waka, sai manzon Allah yace eh akwai, ya kai balaraben kauye a geffan koramar aljanna akwai fararen `yan mata da suke rera waka da sautin da halittu basu taba jin irinsa ba, yace amma fa da tasbihi.

Riwaya ta uku:

مامن عبد يدخل الجنة الا عند راسه ورجليه اثنتان من الحور يتغنين بااحسن الاصوات سمعه الانس والجن ليس بزمار الشيطان ولكن بتمجيد الله وتقديسه

Babu wani bawa da zai shiga aljanna face wurin kansa da kafafunsa akwai matan aljanna biyu da suke rera waka da mafi kyawun sauti da mutane da aljannu suka taba ji bawai da garayar shaidan ba sai dai cewa da tsarkake Allah da girmama shi.

Shin wadannan riwayoyi sun inganta, me ya sa ba za rera waka a aljanna da kayan rera waka na zamani ba, mene ne ya sa sai kadai da tasbihi da girmama Allah kadai, muna bukatar Karin bayani.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Duniya da lahira kowaccen sun a da na ta irin yaren, abinda yake duniya inuwa ce da kama da wane baya wane, amma abinda yake a lahira hakika ce daga tabbatattun abubuwa, ita duniya jarrabawa ceda kyawawa da miyagu da alheri da sharri  akwai abinda cikinsa akwai haramun misalin wake-waken zamani (music) an cika da hakane don baiwa mutum damar yin zabi da kansa, domin banbance gurbatacce daga tsaftatatacce, Salihi daga Azzalumi, daga wanda ya kasance kan hanyar Annabawa yana bin ubangiji ya kuma kasance cikin ma’abita farin ciki daga `yan aljanna, da kuma wanda ya zabi hanayr Iblis shi yana daga marasa arziki da farin ciki kuma yana daga ahalin wuta, sai dai cewa ita aljanna gida na azurtattu da tsarkaka, cikin babu kayan haramun idan aka samu waka cikinta to dole ta kasance waka ta halal wacce take kasancewa tasbihi da girmama ubangiji , cikin aljanna akwai abinda rai yake sha’awa, idan mumini yayi shaukin wake-wake lallai zai samu sai dai cewa wake-waken da suke dacewa da aljanna bawai na duniya ba.

Daga karshe muna rokon Allah da bamu dama mu kasance cikin auzrtattu `yan aljanna mu bar aikata haramun cikin jin waka da yinta cikin wannan duniya domin mu amfani hakan a ranar lahira daga ni’imomi na har abada cikin aljanna da koramu cikin matsugunin gaskiya wurin sarki mai ikon yi, ya ubangijin talikai.

Tarihi: [2019/7/4]     Ziyara: [507]

Tura tambaya