mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Me ake nufi da fadin: duk sanda hijabe ya yaye haske na karuwa?


Salam Alaikum. Kun fadi wata kalma mai daraja (duk sa’ilin da hijabi yay aye haske na karuwa) ku taimaka mana da Karin bayani Allah ya saka muku da alheri.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
Yayewar hijabi na kasancewa da barin aikata zunubi da makaruhi da shubuha, sannan a lazimci aikata mustahabbai kari kan wajibai, sannan dabi’antuwa da dabi’un Allah ta hanyar wurgi da watsi da munanan siffofi da yin ado da kyawawa ababen yabawa har bawa ya kai ga matsugunin gaskiya wurin sarki mai ikon yi, su hijabai akwai na duhu mafi bayyanarsu shine son duniya lallai shi son duniya shine jagaban dukkanin kura-kurai, sannan daga cikinsu akwai na haske misalinsu kamar misalin wanda yake kallon surar wata cikin tafki sai yayi tunanin cewa a hakika watan ne yake gani, sai dai cewa idan ya zurfafa kallo ya bincika sai ya gano cewa hoto da surar watan ce ta bayyana cikin tafkin kamar surar wanda yake gaban madubi ke bayyana cikin madubi, sai ya ciratu daga wannan hijabi na hasken farko zuwa haske na biy wanda shina wata

 

Salam Alaikum. Kun fadi wata kalma mai daraja (duk sa’ilin da hijabi yay aye haske na karuwa) ku taimaka mana da Karin bayani Allah ya saka muku da alheri.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Yayewar hijabi na kasancewa da barin aikata zunubi da makaruhi da shubuha, sannan a lazimci aikata mustahabbai kari kan wajibai, sannan dabi’antuwa da dabi’un Allah ta hanyar wurgi da watsi da munanan siffofi da yin ado da kyawawa ababen yabawa har bawa ya kai ga matsugunin gaskiya wurin sarki mai ikon yi, su hijabai akwai na duhu mafi bayyanarsu shine son duniya lallai shi son duniya shine jagaban dukkanin kura-kurai, sannan daga cikinsu akwai na haske misalinsu kamar misalin wanda yake kallon surar wata cikin tafki sai yayi tunanin cewa a hakika watan ne yake gani, sai dai cewa idan ya zurfafa kallo ya bincika sai ya gano cewa hoto da surar watan ce ta bayyana cikin tafkin kamar surar wanda yake gaban madubi ke bayyana cikin madubi, sai ya ciratu daga wannan hijabi na hasken farko zuwa haske na biy wanda shina wata, sannan ya duba ya ga wannan haske na madubi da yake hakaito wata da makamantansa duk da cewa ya kasance hasken wata sai dai cewa hasken rana ne bayan wani lokaci sai ya ga wannan haske ya dusashe ya buya, lallai haskensa daga hasken waninsa yake, Lallai Allah shine hasken sama da kasa, sai dauko daga hasken rana ya zuwa hasken Allah matsarkaki, wadannan hijbai nah aske na jeka na yika ko kuma muce suna tukewa zuwa ga hasken dukkanin haske mai haskaka haske hasken gaskiya girmansa ya girmama.

Tsakanin bawa da duniya mala’ikanta shine duniyar ayyukan Allah akwai hijabai dubu saba’in na haske, sannan tsakanin duniyar malakutiya da tsakanin jabarutiya wacce itace duniyar siffofin Allah da sunayensa akwai hijabai dubu casa’in, tsakanin duniar jabarutiya ya zuwa duniya lahutiya wanda itace mukamin zatin Allah gaibun gaibobi akwai hijban haske da babu wanda ya sansu sai Allah matsarkaki da masu zurfafa ilimi Muhammad da iyalansa tsarkaka (as) wannan duniya tana komawa zuwa ga ahalinta da waliyai Salihai ni bana daga cikinsu.

Sarai Allah ya azurta ni da aiki nagari ya sanya ni in ji kamshin iskar Salihai da aljannarsu da ni’imarsu, lallai na karar da rayuwa cikin takaitawa da gazawa ina turbaya ina ita ina kaiwa ga matsayin mukami da daukaka irinta tauraron Surayya, ia za hada digon ruwa da teku, ina za a hada kwayar zarra da katon dutse, sama taiwa yaro nisa?

Tarihi: [2019/7/4]     Ziyara: [684]

Tura tambaya