mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Sakin aure ta hanyar telefon


Salamu Alaikum:
Ina fatan samun amsar tambaya ta.
Shin ya halasta ayi saki da ta hanyar wayar telefon da Kalmar ke sakakkiya ce cikin auren mutu’a saboda mijina ya kasance cikin fushi kai ina tsammanin ma yana cikin maye ya aikata hakan sai kuma daga baya muka dawo daidai kamar yadda muke a gabanin faruwar al’amarin, yanzu bayan haka na dauki ciki da shi sai yake ce mini wannan `dan da kike dauke da shi `dan haramun ne saboda ni na sake ki ta hanyar aiko miki da wasika ta telefon… ni da shi ma’aurata ne da auran mutu’a da zuruf dinsa bisa abin da yake fadi, sai dai cewa a wajen mutane ni da shi muna tare tsahon shekaru hudu muna zaune lafiya lau.

 

بسم الله الرحمن الرحیم

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Cikin aure mutu’a sigar saki da rabuwa bata kasance daga fadin na sake ki ba wannan kalmar tareda sharuddanta tana kasance cewa sigar saki da rabuwa kadai cikin auren dindin, kadai dai sigar saki da rabuwa da juna cikin auren mutu’a shi ne fadin (na kyautar miki da kwanakin) saboda haka `danki `dana na halaliya sannan abin da ya fadi kadai dai ya jahilci mas’alar me ko kuma yana son cutar dake, Allah ya gyara masa halinsa ya bashi guzuri da ilimi da ma’arifa sannan ya shiryar da shi damu zuwa ga abin da cikinsa alheri yake.

Allah ne abin neman taimako. 
Tarihi: [2017/12/18]     Ziyara: [753]

Tura tambaya