mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Bayan ubangiji mai tausayi ya datar dani da haskakuwa da hasken wilaya da rungumar mazhabin iyalan manzon Allah (s.a.w) amma tare da hakan ina fama da fuskantar tsoro daga Allah, yay azan iya kubuta daga wancan tsora da razani da yanayi da yake yawan biji

Salamu Alaikum. Mu muna daga cikin wadanda suka yi istibsari daga sunnanci zuwa hasken Muhammad da iyalansa tsarkaka, sai dia cewa mun rigaya mun tasa cikin `yan darikar tijjaniya tarbiyarmu ba ta nun aba kan tarbiyar manzhabin Ahlil-baiti, tambaya ta anan shine ta yaya zan iya riskar da ayyukan da suka gabata kan wancan tsohuwar mazhaba da kuma gyara su, domin na tasoi cikin wancan tunani ina son karkade duk wata kura da inuwar wancan tsohuwar matafiyar, domin akwai gurbatattattun akidu kunshe cikinta da suke bibiyata na kasa rabuwa da su, misalin raya cewa Allah yana zaune a kan karaga a samaniya da daidai makamantansu, sai da yawa na kan bakin ciki da nadama kan kasantuwar rashin samun wanda zai nusantar da ni da tarbiyantar dani tarbiyar gidan manzon Allah (s.a.w) da iyalansa tsarkaka, ko yaushe sai in ta jin kaina ma’abocin babban zunubi bisa gazawa ta cikin sanin Allah yadda ya kamata

Salamu Alaikum. Mu muna daga cikin wadanda suka yi istibsari daga sunnanci zuwa hasken Muhammad da iyalansa tsarkaka, sai dia cewa mun rigaya mun tasa cikin `yan darikar tijjaniya tarbiyarmu ba ta nun aba kan tarbiyar manzhabin Ahlil-baiti, tambaya ta anan shine ta yaya zan iya riskar da ayyukan da suka gabata kan wancan tsohuwar mazhaba da kuma gyara su, domin na tasoi cikin wancan tunani ina son karkade duk wata kura da inuwar wancan tsohuwar matafiyar, domin akwai gurbatattattun akidu kunshe cikinta da suke bibiyata na kasa rabuwa da su, misalin raya cewa Allah yana zaune a kan karaga a samaniya da daidai makamantansu, sai da yawa na kan bakin ciki da nadama kan kasantuwar rashin samun wanda zai nusantar da ni da tarbiyantar dani tarbiyar gidan manzon Allah (s.a.w) da iyalansa tsarkaka, ko yaushe sai in ta jin kaina ma’abocin babban zunubi bisa gazawa ta cikin sanin Allah yadda ya kamata.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Daga cikin abin da babu shakku cikinsa shine Allah matsarkaki yana yafe baki dayan zunubai duk yanda suka kai in banda tarayya da Allah, lallai ita shirka zunubi ne mai girman gaske da bai yafeta kuma tana janyo gurbatar dukkanin ayyuk, amma dukkanin wanda ya kasance mai dayanta Allah amma tare da hakan sai ya aikata zunubi kai da zai aikata zunubin mutum da aljan sannan daga baya ya tuba taubatun nasuha to lallai Allah zai yafe masa ya kuma gyara lamarinsa da rayuwarsa, ya sauya munanan ayyukansa da kyawawa, ya daukaka darajar kyawawan ayyukansa aljannoni madaukak, tare da misalin wnanan rahama ta ubangiji mai yalwa shin akwai wani debe tsammani da zai ragu ko kuma wasu burbushen gurbatattun akidu da suka gabata da guraben miyagun ayyuka da suka gabata?!! Haihata-haihata faufau bari dai dan’uwa kai kana cikin rahama sai dai kawai shaidanu ba zasu taba laminta ka kasance cikin hutu da nutsuwa ba kana mai samun kwanciyar hankali a zikirin Allah, sai ka same su suna bakin kokarinsu cikin bata zukata da rura wutar abubuwan da suka gabata  har ta kai ga bawa ya fara jarrabtuwa da debe tsammani daga rahamar Allah ya zamanto ya kara komawa rundunar shaidani, kiyi bakin iyawarki yake `yar’uwa  `yata kan gani kin yi galaba kan shaidan ta hanyar dogara da Allah, da riko da kalmarsa madaukakiya da karfaffar igiyarsa Muhammad da iyalansa (as) ka da ki manta da rabonki daga duniya ki sanya ta wurin shukar don girba a lahira, Allah ya jikan bawan da ya Ankara da inda yake, ya kuma fadaka kan ina zai je, da kuma me ake nema daga gareshi? Wanne abu ne zai fitar da shi daga addininsa, farin ciki ya tabbata ga wanda ya san kansa ya kuma san ubangijinsa, ya san kowanne abu, sannan mafi alehrin mai tarbiya shine Allah kamar yanda annabi Mustafa (s.a.w) ya fadi:

 (ادّبني ربّي فأحسن تأديبي)

Ubangijina ya tarbiyantar dani ya kuma kyawunta tarbiyata

Ana kiran hakan da darikar uwaisiyya, hakika Uwaisu Karni bai ga annabi (s.a.w) lokacin rayuwarsa sai dai cewa ya kasance daga masoyansa, akwai wadanda suka kasance tare da annabi (s.a.w) sai dai cewa sun cutar da shi sai la’anar Allah da azabarsa mai radadi ta game da su. Kamar yanda ya zo cikin littafin Bukhari, sai ka lura.

Sannan jin takaitawa da gazawa da kike yi abune mai matukar kyawu lallai ya zo cikin addu’a:

(اللّهم لا تخرجني من حدّ التقصیر)

Ya Allah ka fitar da ni daga haddin gazawa.

Lallai duk yanda bawa yakai cikin ibada lallai ba zai gushe ba yana mai ganin kansa gajiyayye mai zunubi kamar yanda ya zo cikin Du’a’u Kumail ta maulana sarkin muminai Ali (a.s) ki roki llah madaukaki da ya datar da ke da dukkanin masoya iyalan manzon rahama (s.a.w)

Karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai

Tarihi: [2018/12/30]     Ziyara: [731]

Tura tambaya