mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

MENENE ILLA CIKIN AUREN ALI DA FATIMA (AS) SHIN UMARNIN UBANGIJI NE

MENENE ILLA CIKIN AUREN ALI DA FATIMA (AS) SHIN UMARNIN UBANGIJI NE?
2-Shin riwayoyin da aka rawaito daga Ahlus-sunna karbabbu ne daga fuskanin farkon wanda zai fara shiga aljanna ita ce Fatima?
3- shin Mufaddal da Hisham da Zuraratu raunana ne cikin riwaya?
4-shin kun samu sunan mutumin nan da ya zo a riwayar (ani mutum ya zo) mutumin da ya zo kabarin Annabi (s.a.w) yana tawassalin domin neman ruwa.
5- shin ya kona kofar Fatima da gaske, saboda akwai wadanda suke shakku kan haka?

 

2-Shin riwayoyin da aka rawaito daga Ahlus-sunna karbabbu ne daga fuskanin farkon wanda zai fara shiga aljanna ita ce Fatima?

3- shin Mufaddal da Hisham da Zuraratu raunana ne cikin riwaya?

4-shin kun samu sunan mutumin nan da ya zo a riwayar (ani mutum ya zo) mutumin da ya zo kabarin Annabi (s.a.w) yana tawassalin domin neman ruwa.

5- shin ya kona kofar Fatima da gaske, saboda akwai wadanda suke shakku kan haka?

 

da sunan Allah mai rahama mai jin kai

amsa kan tamayarka ta farko: zabin Allah bai kebanta da Annababta da imamanci kadai ba bari dai ya gudana cikin misalin sunayen mutanen cikin bargo (a.s) hakika Allah ya zabi sunayensu ya tsago su daga sunayensa kamar yanda ya zo cikin tabbatattun hadisai , sannan ya zabi auren Sarkin muminai (as) daga shugabar mata Fatima Zahara (as) saboda ya zo cikin hadisi ingantacce cewa (ba don Ali ba da Fatima ba ta da tsaran da zata aura) Biharul-Anwar j 45, saboda haka su tsaran juna da suka daidaita da juna cikin ba’arin wasu mukamai, sannan idan Sarkin muminai Ali (as) ya kasance shi ne nafsun Manzon Allah (as) da nassin ayar mubahala to lallai Fatima Zahara (as) ita kuma ruhin Manzon Allah (s.a.w) kamar yanda ya zo cikin hadisi (Fatima ruhina ce wacce da take tsakankanin geffana guda biyu, idan Manzon Allah (s.a.w) yayi mi’iraji da ruhinsa haka zalika yayi da nafsunsa saboda haka Ali da Fatima (a.s) surori ne guda biyu ga hakika guda daya  wacce ake kira da hakika Muhammadiya ita nafsu ce gud adaya wacce ta gangaro daga gud adaya rak da hukuncin ka’idar wahid kamar yanda haka ya tabbata wurin masana Falsafa, sannan ya halittar mata mijinta daga gareta, anan ne fa farkon aurantaka ta fara cikin duniyar mala’ikantaka da gaibu da Mala’ul A’ala da Aliyu da Fatima (as) haka al’amarin yake cikin duniyar Malak da Shahada da duniyarmu, anan sirri daga sirrikan aurensu wanda ya kasance da umarnin Allah matsarkaki yake bayyanuwa ga wanda yake karanta wannan maudu’i yake kuma tuhumar shi’a da aikata gullanci sakamakon rashin sanin sakafar shi’a wacce take bayyanar maka abin da yake sanya kirazan wadanda suka narke cikin soyayyar Ali da Fatima (as) lallai shi ranar lahira bayani zai zo: ina masoya Fatima sai kuma ka ji sauti ya daidaitu da shi ya fiti ya dagawa: ina masoya Ali ina masoya Muhammad ina masoya Allah, lallai Sarkin muminai (as) ya ce: ni bawana ne daga bayin Muhammad Allah matsarkaki yana cewa: Muhammad bawansa ne Manzonsa ne, babu banbanci tsakaninka da su face dai su bayinka ne baresu da mannesu duka na hannunka kamar yanda ya zo cikin Du’a’u

Rajab cikin madaukakin hadisi: (ba da ban kai ba ya Muhammad da ban halicci falakai ba da ba don Ali ba da ban halicceka da ba don Fatima ba da ban halicceku ba)

Hakan ya kasance ne daga banin sinkiya tsakanin illa da ma’aluli kamar yanda na yi bayani filla-filla cikin littafin (Fatima Zahara Sirrul Wujud)

 

Amsarka kan tambaya ta 2: shiga aljanna yana daga al’amuran nsibiyya cancantuwa ba ta kasance saki babu kaidi a nan bari dangantaka ya zuwa al’amari yana kasance da farko wani lokaci ga al’amari na daban, alal misali ana iya cewa da farko wanda zai fara shiga aljanna daga matai ta ce Fatima Zahara (as) daga maza kuma Ali (as) sai dai cewa kuma fa ana nufin bayan Manzon Allah (s.a.w) ya shiga babu karo cikin haka sabida mas’alar nisbiya ce ba mudlaka ba ce tsantsa, misali nawa muke da shi daga haka cikin Akidu a Fikhun muslunci.

Sannan shi hisabin da lissafin lahira ya sha banban da na mu lissafin na gidan duniya, ta iya yiwuwa a tunanin haka ya kasance daga nau’in wulakanci sai dai cewa kuma ya isar ma Allah ya nufi bayyanar da matsayin Fatima (as) hakan karkashin umarnin Manzon Allah (s.a.w) ace ta shiga aljanna gabanin shigarsa shin cikin hakan akwai wulakanci?

Alal misali mahaifi yana son bayyanar da matsayin dansa cikin umarninsa ya umarce shi da shiga gida gabanin shigarsa shin yanzu za a kirga hakan matsayin wulakanta mahaifi? Ko kuma dai akasi hakan yana ishara zuwa ga girman matsayin dan.

 

Amsar tambaya ta uku: yana daga cikin tabbatattun abubuwa cikin ilimin Diraya cewa wadannan manya mutane suna daga Ashabul ijma kuma su Sikkatul Sika ne kuma Sabtu-Sabtu, kuma su suna daga Hawariyan Sahabban A’imma (as) kuma wadanda suka aminta da su kan sirrikansu, amma maganar da ta zo kan zarginsu hakika Imamai sun yi bayani sababun hakan, daga cikin sun zarge su ne don kare rayukansu daga abind asuke tsoratar musu daga Azzaluman Sarakunan zamaninsu, idan har ka karanta Fihirisat hakikanin karatu lallai zaka samu sirrin zarginsu ya isar a zahiri, kai dai ka haddace wani abu ne amma kuma abubuwa masu yawan gaske sun faku daga gareka, ubangiji shi ne abin neman taimako.

 

Amsa kan tambaya ta hudu: Allah ya saka maka alheri bisa wannan riwaya da ka amabta daga litattafan `yan’uwa Ahlus-sunna ta yiwu a ambatarwa Umar wata falala daga falaloli sai dai cewa sun gafala kan cewa wannan falala ta sa tana cin karo da abin da Mazhabar `yan Wahabiyawa suka tafi akai wadanda suke ganin hakan matsayin shirka, ta kaka zai yi tawassali da manzon Allah (s.a.w) bayan wafatinsa lallai ai ya rigaya ya mutu bai da ikon yin komai, cikin rubutunka na fahimci cewa baka kana kokarin sanin mutumin ba ne bari dai kana son ishara ya zuw aga falalar Umar bisa tsinkayenka kan Masadir din sunna Allah ne mafi sanin hakikanin lamurra, sai dia cewa kamar yanda ake cewa: (abin da mutum ya boye yana bayyana a kan harshensa da shafin fuskarsa) ina kari kan haka da kuma kalmomin da ske kunshe cikin wasikarsa, ina rokon Allah ya shiryar da kai ya zuwa gaskiya da daidai, tana iya yiwuwa abin da ka ambata ya kasance daga waninka kai ka nufi sanin gaskiya neto anan nima misalinka ne ban san mutumin ba? Rashin sani wani lamari ne da baya cutar da addini.

 

Amsa kan tambayar ta 5: abin da ka ambata daga hadisi daga littafin Ahlus-sunna lallai hujja ne a wurinsu bawai a kanmu sannan kana iya komawa ka duba litattafan babban malami masani dan kasar Lubnan Assayid Jafar Murtada Amili cikin littafinsa mai suna (Zalamatul Zahara Alaihas Salam) da sannu zaka tsinkaya kan hakikanin lamari da abubuwan da suka faru a tarihi da zaluncin da akaiwa Ahlil-baiti (as) haka zalika ka duba littafin Jalalud dini Assuyudi cikin Bahjatul Mardiya kan Sharihin littafin Alfiya cewa Umar ya zo da itace domin kona gidan Fatima (as) sai aka ce masa Fatima fa tana cikin gidan sai ya ce ko da tana ciki?!   

 

Tarihi: [2019/10/1]     Ziyara: [3159]

Tura tambaya