mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Tambaya dangane da ayar muwadda

Salamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu
Akaramakallahu Allama Assayid Adil-Alawi (H)
Ina da wasu `yan tambayoyi gameda ayar muwadda, ayar da manya daga malamai misalign Saduk su kayi la’akari da ita matsayin dalili kan wajabcin soyayyar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu, daidai loakcin da muke samun wasu manya daga Malamai misalin Allama hilli hakama Allama Tabataba’i na wannan zamani suna cewa ayar ta tattaro dukkanin zuriyar Annabi (S.A.W) bawai kadai Ahlil-baiti ba , muna neman Karin bayani daga gareku menene ake nufi daga soyayyar makusanta yaya fadadar soyayyarsu ta zurfafa sannan shine wannan wajabcin soyayya wajabcine na Aklak ko kuma na menene

Salamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

Akaramakallahu Allama Assayid Adil-Alawi (H)

Ina da wasu `yan tambayoyi gameda ayar muwadda, ayar da manya daga malamai misalign Saduk su kayi la’akari da ita matsayin dalili kan wajabcin soyayyar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu, daidai loakcin da muke samun wasu manya daga Malamai misalin Allama hilli hakama Allama Tabataba’i na wannan zamani suna cewa ayar ta tattaro dukkanin zuriyar Annabi (S.A.W) bawai kadai Ahlil-baiti ba , muna neman Karin bayani daga gareku menene ake nufi daga soyayyar makusanta yaya fadadar soyayyarsu ta zurfafa sannan shine wannan wajabcin soyayya wajabcine na Aklak ko kuma na menene?

Idan kuma ayar bata nuni kan wajabcin soyayyarsu shin akwai wani dalili na daban daga Kur’ani da sunna da yake nuni kan haka?

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Ya zo daga ingantaccen hadisi kan ma’anar (Alkurba) makusanta cikin aya mai daraja sune Fatima da da mijinta da `ya`yanta wadannan soyayyarsu wajibi ce a akidance domin tana daga Asalan addini da laziman Annabta da Imamanci, amma ta fuskanci fikihu kasancewar kaunarsu da son su rassa ne na addini daga wilaya da bara’a, amma zuriya wadanda ba Ma’asumai ba wannan yana daga babin alifun din da take danfare da ainun ana girmamata ne alfarmar harafin ainun din, kamar yanda ya zo cikin nassoshi masu tarin yawa sun ma kusa su kai haddin tawatiri, nayi bayani filla filla cikin littafin (Alma’amul fi Takrim Zurriyatil Rasul) an buga shi kuma an sauke shi a sayit din Alawy.net 

Tarihi: [2021/2/20]     Ziyara: [511]

Tura tambaya