b Ina da `da mai tsananin fusata
mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ina da `da mai tsananin fusata

Salamu Alaikum

Gaisuwa ga Sayyid Adil-Alawi (h) da dukkanin mai bada gudummawa a wannan sayit mai albarka

Inada `da `dan shekara biyu da yake da tsananin fushi da shawo kansa yake da wahala, shin ko zaku taimaka mana da wani abu daga ilimin iyalan gidan manzon rahama (s.a.w) domin magance wannan matsala. Allah ya saka da alheri

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Da izinin Allah zai zama alheri zai sauya, kamar yanda ya zo cikin hadisi daga Imam Kazim (as) shine kuyi hakuri ku bishi a sannu lallai shi yaro har zuwa shekaru bakwai yana jin kansa shugaban kansa daga bakwai kuma zuwa 14 zai kasance cikin mukamin tarbiya daga iyayensa daga 14 zuwa 21 zai kasance wazirin mahaifinsa ya zama babban mutum cikin iyali da dangi kamar yanda hakan ya zo cikin riwayoyi.

Tarihi: [2019/1/28]     Ziyara: [580]

Tura tambaya