mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin daga Azzahra (as) aka halicce mu?

Assalamu alaikum, muna bukatan sayyid ko zai taimaka mana da nasiha da kuma cikakken bayani kan hanya ta gari wacce kowa ke muradi kuma zata kaimu zuwa ga Allah da taimakon kan mu, naji a wata jimla wata zama na karatu da kayi kana cewa (طوبى لمن عرف قدر نفسه) wato Albarka ta tabbata ga wanda ya san matsayin kansa, (من عرف نفسه فقد عرف ربه) duk wanda yasan kansa toh yasan uban gijin sa haka kuma (ومن عرف ربه فقد عرف كل شئ) duk wanda yasan uban gijin sa yasan komai, acikin ziyararta mukan ce " اشهد اني طاهر بولايتك" shin wannan shine ake nufi da matsayin kai? Kuma shin mu daga Azzahra (as) aka halacce mu? Na hura ruhina a cikin sa, kuma a wani magana akance azzahra ruhi ta ce wacce ta kasance a tsakani, mala’iku da ruhi suna saukowa gare ta.
Sannan mala’uku acikin wannan zamani na mu na yau suna saukowa wa imama Mahdi (as), shin a zamanin annabin tsira da kuma na Zahra mala’iku suna sauka ne sauka na hakika? Ina neman Karin bayani akan haka.

Da sunan Allah me rahama me jin kai

Allah ne me saukar mana da dukkanin Alheri amma sharrina ke zuwa gare ka, ya Allah duk lokacin da na kalli zunubai na nakan kasance cikin masu na dama, sannan duk lokacin da na kalli rahamar ka nakan sami shauki, wannan shine halin bawan na gari wanda ya kaskantar da kansa a gaban Allah, ba lallai sai ya kasance an sami yanayi guda cikin aiki, duk wanda ya sami kan sa cikin masu yabon Allah da kuma bauta masa wannan shine alama na halin dan adam me mutunci kuma haline na ruhin shi, idan kuma ya sami kansa cikin jahilci da kuma gaggawa wannan na daga halin jiki ne na duniya.

A zamanin azzahra mala’iku da ruhi sukan sauka wa annabin tsira a lokacin da yake raye amma lokacin da yayi wafati sukan sauka ne wa imam Ali, mala’iku sukan sauko wa dukkanion cikakken dan Adam wanda shi mazhar ne na sunayen Allah daga annabi har zuwa waliyan Allah wato wasiyan Annabawa.  

والله العالم

Tarihi: [2016/9/6]     Ziyara: [926]

Tura tambaya